Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ta kashe Naira miliyan 175.5 wajen gyara filayen wasanni guda biyu a jihar.
Kwamishinan Wasannin jihar, Sani Danlami ne ya bayyana haka yayin da yake bayyana nasarorin da ma’aikatarsa ta samu a ranar Laraba.
- Mun kammala duk ayyukan da muka gada – Gwamnatin Katsina
- Katsina za ta farfado da masana’antar sarrafa darbejiya
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta kashe Naira miliyan 111.3 wajen gyaran filin wasa na cikin garin Malumfashi, sai kuma Naira miliyan 64.2 wajen gyaran filin wasa da ke cikin garin Katsina.
Sani ya kara da cewa gwamnati ta yi hakan ne domin farfado da harkokin wasanni a jihar.
Kazalika, ya ce ma’aikatar ta kuma kashe Naira miliyan 9.25 wajen kwashe masu larurar tabin hankali da ke gararamba a kan titunan jihar, sai miliyan 1.57 da aka yi amfani da su wajen mayar da masu gudun hijira zuwa garuruwansu da ke ciki da wajen jihar.