✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Binuwai na sahun gaba-gaba wajen yi wa mata fyade a Najeriya

Matan da aka zalunta ba su da damar su bi hakkinsu ta fuskar shari’a.

Jihar Binuwai na sahun gaba-gaba wajen cin zarafin mata ta hanyar yi wa ‘yan mata fyade, a cewar wata kungiya mai zaman kanta.

Kungiyar mai wayar da kai kan laifukan cin zarafin mata da fyade (SOAR) ce ta bayyana ta haka, ta bakin shugabarta Chinyere Eyoh, a wani taro da ta yi da masu ruwa da tsaki na jihar a ranar Talata.

Shugabar ta ce, alakaluma sun nuna cewa jihar ce ke kan gaba da yawan masu aikata wannan laifi ga ‘yan mata, don haka suka soma yaki da wannan halayyar daga jihar.

Sannan ta ce, duk da wannan mummunan matsayi na jihar, matan da aka zalunta ba su da damar su bi hakkinsu ta fuskar shari’a.

“Wasu daga cikin al’umma ba su dauki wannan cin zarafi a matsayin laifi ba, maimakon a bi hakkin wacce aka cuta, sai iyayenta su zo a sasanta, wanda ya ci dauki alhakinta kuma ya yi tafiyarsa,” in ji Ekoh.

Ita kuwa Beatrice Shomkegh ta Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya murna ta yi da la’akari da yadda aka assasa shirin yaki da cin zarafin yara mata musamman a sansanin ‘yan gudun hijira a jihar.