✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jigon APC ya tsallake rijiya da baya a jihar Edo

Daya daga cikin jigon jam’iyyar APC a jihar Edo Henry Idahagbon, ya tsallake rijiya da baya daga wajen wasu ‘yan bindiga da suka kai masa…

Daya daga cikin jigon jam’iyyar APC a jihar Edo Henry Idahagbon, ya tsallake rijiya da baya daga wajen wasu ‘yan bindiga da suka kai masa hari a ofishinsa.

Henry Idahagbon, mamba ne na kungiyar ci gaban jama’ar Edo (EPM), sannan daya daga cikin na hannun daman shugaban APC na kasa Adams Oshiomhole.

Maharan sun kai wa Henry, hari ne a ofishinsa da ke lamba ta 52b hanyar Siluko cikin garin Benin babban birnin jihar, inda suka rika harbin gidan da ofishinsa yake.

Kafin ‘yan bindigar su kaiwa Henry hari sun shiga wani gidan abinci da ke kusa da ofishin inda suka lalata wasu kayan gidan abincin.