✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jigawa ta samar  da kayayyakin kimiyya a makarantu 8

Gwamnatin Jihar Jigawa ta dukufa wajen samar da kwararrun likitoci da managartan malaman kimiyya, kuma a sakamakon haka ne ta samar da kayayyakin koyarwa ga…

Gwamnatin Jihar Jigawa ta dukufa wajen samar da kwararrun likitoci da managartan malaman kimiyya, kuma a sakamakon haka ne ta samar da kayayyakin koyarwa ga makarantun kimiyya guda takwas domin inganta harkokin koyarwa a jihar.

Gwamnatin jihar ta ce ta kashe Naira miliyan106 da dubu 14 da 155 wajen sayo kayayyakin koyar da ilimin kimiyya da suka hada da Chemistry da Biology da Physic da nufin samar da kwararrun injiniyoyi da malaman kimiya masu nagarta a jihar.

Jawabin hakan ya fito ne daga bakin babban jami’in Cibiyar Kula da shirin (Centre For Edcellence) na Jihar Jigawa Malam Sani Garba a wajen taron raba wa makarantun kayan aiki da aka yi amakarantar Model da ke Dutse a ranar Alhamis din makon jiya.

Ya ce gwamnatin jihar ta kashe fiye da Naira miliyan daya da dubu 849 wajen sayo kayayyakin kimiyyar ga makarantun takwas da aka ware domin fara bai wa malamai da daliban makarantun horo yayin da gwamnati ta kashe Naira miliyan 33 da dubu 794 da 730 wajen gyaran ajujuwan koyar da kimiyya a makarantu hudu daga cikin takwas da suke bukatar gyara domin nazarin kimiyya da kere-kere da koyar da ilimin kwamfuta.

Makarantun hudun da aka yi wa gyara sun hada da GUSS ta Ringim da Dutse Model School da GUSS Fantai da kuma SSS Lautai da ke Karamar Hukumar Gumel.  Yayin da sauran hudun da ba su bukatar gyara sun hada da GGSS Kazaure da GDSS Babura da GDSS Bulangu da kuma GGUSS Gwaram.

Da yake karin haske, Shugaban Makarantar Model da ke Dutse Malam Lawan Adamu Yusuf ya ce nan gaba akwai makarantu shida da za su ci moriyar shirin da zarar an kammala da wadanda aka fara da su.  A cewarsa makarantun sun hada da GUSS Basirka da GUSS Maigatari da GUSS Aujara da GUC Birnin Kudu da GGUSS Malam Madori da GDSS Gwaram.

Malam Lawan Yusuf ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta bullo da shirin ne da nufin zaburar da dalibai su zama masu kwazo wajen harkar ilimi da karatun likita da na injiniya.

Ya ce samar da kayayyakin koyarwa na zamani ya zo a kan gaba, domin ana dab da yin jarrabawar karshe inda ake sa ran dalibai za su yi amfani da wannan dama don ganin sun amfana da shirin.