✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jibi za a rufe Gasar Wasanni ta Kasa karo na 19

A jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu za a kammala Gasar Wasanni ta Kasa Karo na 19 da yanzu ke gudana a Abuja.  Gasar wacce…

A jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu za a kammala Gasar Wasanni ta Kasa Karo na 19 da yanzu ke gudana a Abuja.  Gasar wacce aka fara a ranar 6 ga Disamban nan za ta kawo karshe ne a jibi kamar yadda jadawalin shirya gasar ya nuna.

Jihohi 36 ciki har da Babban Birnin Tarayya Abuja ne suke fafatawa a wasanni daban-daban 37.  A da ana yin wasanni 25 ne amma a bana aka kara suka zama 37.  Sannan kimanin ’yan wasa dubu 10 ne suke fafatawa a gasar.

Wasu daga cikin wasannin sun hada da guje-guje da tsalle-tsalle, da wasan kwallon tebur da judo da Chees da kwallon kafa da damben gargajiya da damben boksin, da kwallon kwando da kwallon badminton da sauransu.

Da farko an shirya Jihar Kuros Ribas ce za ta dauki nauyin gasar amma ganin yadda jihar ba ta shirya ba, ya sa Gwamnatin Tarayya ta kwace gasar inda ta mayar wa Abuja, kamar yadda Ministan Matasa da Wasanni Barista Solomon Dalung ya sanar da manema labarai jim kadan da fara gasar ta bana.

A ka’ida ana gudanar da gasar ce duk a bayan shekara biyu, amma a wannan karo an dauki tsawon lokaci ba a gudanar da ita ba.  A shekarar 2012 ce Jihar Legas ta dauki nauyi kuma tun daga wancan lokaci kimanin shekara 6 ba a sake yi ba sai a bana da ake yi a yanzu a Abuja.

A jibi Lahadi ne za a sanar da jihar da za ta dauki nauyin gasa mai zuwa da ake sa ran yi a shekarar 2020.

Manyan baki ciki da wajen Najeriya ne ake sa ran za su halarci bikin rufe gasar ciki har da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Ministan Matasa da Wasanni Barista Solomon Dalung da sauransu.