✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jibi Manchester United za ta hadu da Leicester City

A shirye-shiryen tunkakar gasar firimiya ta Ingila ta bana, a jibi Lahadi ne kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta kara da ta Leicester…

A shirye-shiryen tunkakar gasar firimiya ta Ingila ta bana, a jibi Lahadi ne kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta kara da ta Leicester City a kofin da ake kira FA Community Shield.
Manchester United ta kai wannan matsayi ne bayan ta lashe kofin kalubale na Ingila a bara yayin da Leicester City kuma ta kasance zakara a gasar rukunin firimiya na Ingila a karon farko a bara.
Wasan zai gudana ne a filin wasa na Wembely da misalin karfe hudu na yamma agogon Najeriya. Kamar kullum wannan wasa shi zai bude kofar gudanar da kakar wasa ta bana da ake san ran farawa a ranar Asabar 13 ga wannan wata da muke ciki. Tuni dukkan kungiyoyin biyu suka kintsa don ganin sun samu nasarar lashe wannan faranti mai dadadden tarihi.