✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jibi Madrid da Madrid za su yi karon-batta

A bangaren gasar rukunin La-Liga ta Sifen kuwa, a jibi Lahadi ne za a yi karon-batta a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid da…

A bangaren gasar rukunin La-Liga ta Sifen kuwa, a jibi Lahadi ne za a yi karon-batta a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid da ta Real Madrid.

Kamar yadda jawabin wasan ya nuna, za a yi wasan ne da misalin karfe 3 da kwata na rana agogon Najeriya a filin wasa na Atletico.

Shi ma wasa ne da ake sa ran masoya kwallon kafa za su yi cincirindo a gidajen kallon kwallo don ganin yadda wasan zai kaya.

Kawo yanzu kulob din FC Barcelona ne a saman teburin gasar da maki 76 sai Atletico Madrid ta biyu da maki 67 sai Real Madrid ta uku da maki 63 sai balencia ta hudu da maki 62.

Idan Atletico ta samu nasara a wasan za ta ba Real tazarar maki bakwai ke nan, amma idan Real ce ta doke Atletico zai zama saura maki daya kenan a tsakaninsu.

Tuni kocin Atletico Madrid Diego Simeone da na Real Madrid Zinedine Zidane suka shirya don tunkarar wasan.