✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Janten dodon kodi

Dirar da’irar dodon kodi Damun dawon modar modi dandanon dumame dadi dokin dirkaniyar kidi dan mazari na ziryar kadi   Zogi radadi Toshewar mafitsara ba…

Dirar da’irar dodon kodi

Damun dawon modar modi

dandanon dumame dadi

dokin dirkaniyar kidi

dan mazari na ziryar kadi

 

Zogi radadi

Toshewar mafitsara ba dadi

Matsala ce ke naman kaiwa badi

Bokan Turai na yi mata barbadi

Alluran magunguna masu wuyar fadi

 

Tsargiya ce

A matse-matsi aka tantance

Wurin tsilla fitsari zai kece

Al’umma na ta ce-ce-ku ce

Masana ga xulli nan ku sunce

 

Mahukunta ka da a yi na-kasa

Mu kasa mu kwashi kashi

’Yan dugwi-dugwi na shan kashi

Wasu ma sun yi yaushi

Ingancin uwar jiki za ta nakasa

 

 

Garkuwar mafitsara

xoda da hanta ta tatattara

Bokan Turai

Ga aikin ceton rai

A taimaka jama’a su sarara

 

Fitsarin jini

Kumburin hanta yai tsanani

xoda kan samu lahani

Cuta bat a lamuni

Lallai a kawo magani

 

A birnin Shehu

Mutane na ta ihu

Kumburin mafitsara kamar huhu

xoda na kan sahu

A kawo magani buhu-buhu

 

Hawan-san Maiwa

Karkarar masu dangi a Dange

Kula da uwar jiki sai an dage

A yi ta maza kamar dage

Lallai a daina nawa

 

damarar daure dodon kodi

Dodon dumin kaudi

Dawurwurin durwan dindi

Dawo daga dandi

A dauki matakan fatattakar xi fadi

 

Karkarar masu cim-makara maiwa da ke yaren Hau-hau wajen hawan sa na sa-in-sa da janten dodon kodi da ke tamke mafitsara, ya illata xoda da jigata hanta kamar yadda binciken Bokan Turai ya haxxaxe xexe-da-xexe. Al’ummar da ke fama da laulayin janten dodon kodi na da dangi a xaramar Hukumar Dange da ke Jihar Mujadaddi.

Shi ko me mahukunta a birnin Shehu Mujadaddi ke tsuwurwurtawa don ganin an dauradamarar tamke wannan cuta da ta dirkako a turke? Shin ta taxaita ne ga Hausawan cimakar maiwa ko har na da acca da iburo da masara da dawa da gero? Ko ma dai wace amsa mahukunta suka bayar ni dai nasan matuxar aka yi sako-sako wajen shawo kan cututtuka irin wadannan to za su ci gaba da yado fiye da yadiya.

Lallai masana su hada xarfi da xarfe wajen tantace musababbin wannan cuta don ka da a ci gaba da ta’allaxa wa dodon kodi, alhali dodon mutum mai yawan kauci ne ke da babban laifi wajen yin sakaci da sakarcin xin gudanar da bincike a kan kari.

Batu na ingarman xarfen xarafan titin kwangiri tarragon layin dogo, ko da an bai wa mazauna karkara magunguna buhu-buhu sun kwankwada sun yi nata, har ingancin uwar jikinsu ta dawo sumul xalau, ai akwai yiwuwar a koma gidan jiya matuxar ba a himmatu ka’in da na’in wajen tsaftace muhalli ba. Wajibi ne a yi mai yiwuwa don shawo kan cbututtukan da ke yaduwar yadon yadiya a karkara da birane, jinda suka yi kane-kane suna cutar da mutane.

Haurobiyawa kowa ya bayar da gudunmuwarsa wajen warware tsilli-tsillin matsalolin da suka yi wa al’umma katutu, kafin su xulla mana kutu-kutu, su tsire mu da tuntu, har laulyin jiki ya tsananta babu hutu. Ni dai wannan shi ne sautuna ka da ku ce na cika taratsin yawan agana. Ku sani dai buxuta ce ta taso kan lallai mu gana, ta yadda za mu samu majingina.

Da zarar bokayen Turai sun sha ku basilla ga banza, to ku nanata musu buxatarku ta fadakarwa. Sun bambance muku fari da baxi. Batun ingarma a yi shi da wando a lallaba a yi wa lange-lange mai ramar xeta bujen xarfe. Kai akwai ma buxatar a yi muku faskaren ma’anoni kan nabin da kimiyya ta gano cikin yaren  Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sain-sa ba. Sannan a bi kowace farfajiyar koyon watsattsake da buda wagagen litattafai da ke karkara don nusar da al’umma abin da ya kamata su fara aiwatarwa kafin su fara neman agaji, don gudun kutsa kai cikin xungurmin daji.

A daura damarar daure DIRAR DA’IRAR DODON KOdI kafin ta zarta makadi da takun rawar kidi, ni kuwa in yi ta fafutikar cika ku da kaudi. Shi kuwa Bokan Turai ya yi ta lasa muku magungu a kamar madi wani ma babu dadi, har ku daina jin zogi da radadin janten jaye-Jayen dodon KOdI  nan da zuwa BAdI. A dai ci gaba da BARBAdI, da DAdI, BA DAdI, NI DAI INA YI MUKU GARGAdI. Muna neman Mai-duka ya yi mana BUdI. Domin tabbas samun warakar al’umma zai cusa mini ZAKWAdIN ZUMUdI yadda zan ji dadin murtguda baki wajen  biro da kowane irin CUKUdI-CUKUdIN cutar da Haurobiyawa.

Cikakken batu game da wannan cuta da ta faskara na nan a shafin jaridar Dalilin-taronsu ta ranar sili da tukunyar dambu ga Yawon-wulli na shekara ta dubu xaramin lauje da sili da kwanciyar magirbi. Sai a yi xoxarin baje na-mujiya, don fasko yadda wannan gagarumar matsala ta auku ko ta auka wa al’ummar karkarar HAUSAWAN CI-MAKAR MAIWA.

’Yan makaranta masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai da mujallu da maxalu da jaridu a farfajiyar dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar xasar Haurobiya, ya zama dole a kanmu mu yi kira ga Gwamna gwarangwam na birnin shehu Mujadaddi ka lallai ya xara xaimin zama MAJIDAdI  ga al’umma, ta yadda zai shawo kan DODON KOdI da ya yi wa mutanen karkara da’ira da dirar mikiya, tun kafin a fara kayya-kayya!