✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyu da yawa matsala ne

A halin yanzu dai an kammala zaben Shugaban Kasa da na ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa da aka gudanar ranar Asabar da ta wuce kuma har…

A halin yanzu dai an kammala zaben Shugaban Kasa da na ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa da aka gudanar ranar Asabar da ta wuce kuma har an bayyana sakamako kowa ya san matsayinsa.

Sai dai kuma ya kamata a yi nazarin yadda zaben ya gudana da nufin gyara kura-kuran da aka samu a zabubbukan don gaba.

Babbar matsalar da ta taso a zaben da ya gabata ita ce ta yawan jam’iyyu, domin jam’iyyu saba’in da uku ne suka nuna sha’awarsu ta fitar da ’yan takarar Shugaban Kasa, saboda haka dole aka fitar da takardar jefa kuri’a mai tsawo saboda jam’iyyun na da yawa.

Sakamakon yawan da jam’iyyun ke da shi ne, masu zabe, musamman mata da tsofaffi, suka samu matsala sosai wajen gano jam’iyyar da suke so su ba kuri’arsu, dole sai da aka taimaka wa wadansu, amma duk da haka wadansu sun tafka shirme, inda suka dangwala wa wata jam’iyyar da ba ita suke nufi ba. Shi ya sanya a lokacin kidaya wasu kananan jam’iyyun suka samu kuri’u masu yawa duk cewa ba su da ’yan takara, domin sun janye sun bar wa daya daga cikin manyan jam’iyyun.

A lokacin da ake da jam’iyyun da ba su wuce biyar ba ma an samu matsala ballantana yanzu da ake da jam’iyyu casa’in da daya, kuma hukumar zabe ta ce bayan zabe za ta ci gaba da yi wa wasu rajista.

Tsarin mulki ne ya bayar da damar yin rajista ga duk wata kungiya da take son rikidewa ta zama jam’iyyar siyasa idan ta cika ka’idojin da aka gindaya.

Idan ta samu rajistar kuma hukumar zabe za ta rika ba ta kudi kamar yadda sashi na 91 (2) na Dokar Zabe ya tanada, inda aka nuna cewa za a rika raba kashi 30 cikin 100 na kudin da za a tallafa wa jam’iyyun da aka yi wa rajista ba tare da bambanci a tsakaninsu ba. Sauran kashi 70 kuma za a rika rabawa ne ga jam’iyyun da suke da ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa, inda za a raba kudin daidai yawan ’yan majalisar da kowace jam’iyya take da su.

Bincike ya nuna cewa daga shekarar 2003 zuwa yanzu hukumar zabe ta raba wa jam’iyyun siyasa  biliyoyin Naira a matsayin tallafi. Wannan ne ya sanya kungiyoyi da dama suke ta kokarin rikidewa su zama jam’iyyun siyasa domin samun miliyoyin Naira a matsayin tallafi daga hukumar zabe.

Idan an lura za a ga cewa ba don samar da dandalin tsayawa zabe ga ’yan takara ne da dama daga cikin jam’iyyun suke ba, suna neman rajista ne kawai domin su rika samun kudin da hukumar zabe take raba wa jam’iyyun siyasa.

Haka kuma da dama daga cikin shugabannin jam’iyyun suna yin amfani da jam’iyyun ne domin su samu alfarma daga manyan jam’iyyun, inda suke tsayar da ’yan takara daga baya kuma sai su janye su su ce sun bar wa wani fitaccen dan takara saboda a ba su wani abu, ko kuma idan ya ci zabe ya ba su mukamai.

Irin wadannan jam’iyyun kuma suna shiga takara ce domin idan an samu matsala a takardar zabe, misali an manta da wata jam’iyya a takardar ko tambarinta, sai su tayar da kayar baya sai an zauna da su an ba su wani abu, ko su je kotu su sanya a rushe zaben. Kamar yadda wata jam’iyya mai suna AAC ta yi a wannan zaben da aka yi, inda ta yi korafin cewa ba a sanya tambarinta a takardar jefa kuri’a ba a Jihar Legas. Yanzu dole sai an zauna da ita domin a sasanta ko kuma ta jawo soke zaben.

Saboda haka kamata ya yi a rage yawan jam’iyyun nan domin ba su da wani amfani sai dai haifar da rudani, saboda suna ruda mutane a lokacin zabe. Ana kafa su ne ba don kishin kasa ba sai domin kishin aljihun wadansu  kawai.

Idan aka ci gaba da yi wa irin wadannan jam’iyyun rajista za a wayi gari wata rana takardar jefa kuri’a za ta zama littafi ne guda da mai jefa kuri’a zai bude yana neman jam’iyyar da yake so ya jefa wa kuri’arsa,  wanda hakan zai kara haifar da bata lokaci a yayin zabe, domin mai zabe zai dauki lokaci wurin neman jam’iyyar da zai dangwala wa kuri’a kuma za a dauki lokaci wurin kidaya, sannan sai an yi amfani da babban daro a matsayin akwatin zabe, wanda zai haifar da matsala wajen dauka zuwa rumfunan zabe da ke birane da kauyuka, haka kuma bayan an kammala zabe daukar akwatunan za ta zama wani babban aiki.

Kamata ya yi a yi gyara a dokar yi wa jam’iyyu rajista yadda zai kasance duk jam’iyyar da aka yi zabe ba ta samu Gwamna ba, to a soke rajistarta, domin ta hanyar Gwamna ko Shugaban Kasa ne jam’iyya za ta iya aiwatar da manufofinta da ta tsara don inganta rayuwar al’umma, hakan zai sa kungiyar da ta san ba ta da karfi ba za ta kashe kudinta wajen neman rajista ba, domin ta san a karshe asara za ta yi. Ta haka za a samu raguwar jam’iyyun zuwa adadin da ya dace.