Jam’iyyar LP ta ce ita ba jam’iyyar shafukan sada zumunta ba ce saboda tana da masu zabe kimanin miliyan 22 a fadin Najeriya.
Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar na kasa, Kwamared Arabambi Abayomi, ne ya bayyana haka a Legas, inda ya ce za su ba ‘yan Najeriya mamaki a zaben 2023.
Arabambi ya kuma ce, ‘yan Najeriya na da burin kawo sauyi ganin yadda jam’iyyar APC mai mulki ta gaza cim ma burin ‘yan kasar.
“Mu ba jam’iyyar kafafen sada zumunta ba ce. Mutanen da suke gudanar da tarukanmu a fadin kasa suna da yawa.
“Mun bullo da sabon al’amari, jam’iyyar siyasa da ba a saba gani ba wacce za ta kawo wa kasa ci gaba daga abin da muke ciki a halin yanzu.
“Kamar yadda nake magana a yanzu, da kungiyoyin da suke goyon bayan jam’iyyarmu da wadanda suka yi rajistar ta hanyar lambobin wayarsu, muna da mutum miliyan 22 da ke tare da mu.
“Kuma muna sa ran samun karin wasu kafin watan Disamba me zuwa.
“’Yan Najeriya na fatan samun sauyi; sun sha wahala sosai kuma sun san wanda suke so ya jagorance su. Ka ga a duk fadin Najeriya harkar ta yi yawa domin Peter Obi shi ne kadai dan takarar da al’ummar Najeriya suka amince da shi. Wadanda ‘yan Najeriya ne ke neman su kawo canji mai kyau,” inji shi.
Ya kuma bukaci gwamnatin APC da ta shirya ficewa daga ofis a 2023, inda ya ce nada masu katin zaben wasu jam’iyyu da tsofaffin ‘yan takara a matsayin Kwamishinonin Zabe ba zai hana jam’iyyar APC shan kaye ba.
Abayomi, ya kuma yi amfani da damar wajen gabatar da Gbadebo Rhodes-Vivour a matsayin dan takarar Gwamna na jam’iyyar a Legas.