✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar OAU ta dakatar da malami kan lalata da daliba

Hukumar jami’ar Obafemi Owolowo da ke Ile Ife a jihar Osun ta Najeriya (OAU) ta sake dakatarwa tare da mika wani malamin jami’ar mai suna…

Hukumar jami’ar Obafemi Owolowo da ke Ile Ife a jihar Osun ta Najeriya (OAU) ta sake dakatarwa tare da mika wani malamin jami’ar mai suna Monday Omo-Elan ga ‘yan sanda bisa zargin yin lalata da wata daliba mai shekara 19.

Mai magana da yawun hukumar jami’ar, Abiodun Olarewaju, ne ya shaida wa wakilin Aminiya faruwar lamarin, inda ya ce sun yanke hukuncin ne bayan wani zama da yammacin ranar Laraba domin ‘yan sanda su ci gaba da bincike a kansa.

Makonni uku da suka gabata ma, jami’ar ta dakatar da wani malami na sashen hulda tsakanin kasashen duniya wato ‘International Relations’ mai suna Misa Olabisi Olaleye, shi ma bisa zargin yin lalata da daliba a sashen.

Mista Olarewaju, ya bayyana cewa hukumomin makarantar a shirye suke su kakkabe duk wani aikin cin zarafi ko kuma lalata daga jami’ar baki daya.

Ya kara da cewa, wannan matakin wani yunkuri ne na tabbatar wa da jama’a cewa, OAU ba za ta lamunci aikata lalata ba sannan kuma ba za ta kyale miyagun da ke aikata hakan ba, ba tare da an hukunta su ba.