Budaddiyar Jami’ar kasa ta Najeriya (NOUN) ta yaye dalibai talatin ’yan kurkuku, wadanda suka samu nasarar kammala samun horo a fannin Kwamfuta a cibiyar jami’ar da ke sashen horar da ma’aikata na CHRD.
Shirin kwas din an gudanar da shi ne a karkashin hadin gwiwar Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kaduna da Kurkukun wadanda aka yanke wa hukuna da ke Kaduna.
Bikin yaye daliban an gudanar da shi ne a harabar Kurkukun wadanda aka yanke wa hukunci da ke Kaduna, kuma ya kasance kaddamar da shirin kashi na biyu na bayar da irin wannan horon a garuruwan da suka hada da Kaduna da Zariya da Kafachan.
Shugaban Jami’ar Farfesa Abdallah Uba Adamu, wanda ya samu wakilcin Daraktan cibiyar Horar da Ma’aikata ta CHRD, Farfesa Grace E. Jonathan ta taya ’yan kurkukun murnar da abokan hadin gwiwar saboda kirkiro da wannan shirin gyaran tarbiyya ta yadda za a dawo da mazauna kurkukun cikin al’umma a kyakkyawan yanayi.
Ya ce kudin karatun ’yan kurkuku a daukacin fadin kasar nan kyauta ne don haka jami’ar ta shirya wannan shirin, wanda ya kai ga samun nasara yaye dalibai kashi na farko da ke zaman kurkuku.
Shugaban ya bukaci wadanda suka kammala samun horon sun fahimci cewa akwai wata rayuwa bayan ta kurkuku. “Bayan kammala zaman wa’adinku, in kun fita daga wannan wurin za ku zama mutane masu amfanar da al’umma, ta yadda za ku karkata akalar rayuwarku wajen yin wasu ayyuka,” inji Adamu.
Tun farko a jawabinta Kwamishinar Shari’a ta jihar, Umma Aliyu Hikima, cewa ta yi ma’aikatar shari’a ta bullo da shirin ne don karfafa ’yan kurkukun su samu madogara mai muhimmanci da za ta taimaka musu su zama managartan mutane bayan sun fice daga kurkuku.
Ta ce shaidar karatun za ta kara taim a musu wajen inganta kimarsu bayan sunm shiga cikin al’umma.
“Wannan shirin a yanzu wani sashe ne na gyaran tarbiyyar fursunonin da zai taimaka wa masu zaman kason su daidaita rayuwarsu tsakanin hukuncin da aka yi mysy da kuma dabarun gyaran halayya lokacin da suke tsare.
“a wajen gudanar da shirin, Ma’aikatar shari’a ta Jihar Kaduna tare da hadin gwiwar gidajen kurklukun Kaduna, sun dora wa Cibiyar Horar da Ma’aikata ta Budaddiyar Jami’ar kasa ta Najeriya “NOUN” nauyin horar fursunonin 30 fasahar sarrafa kwamfuta.
“Ma’aikatar shari’a ta kammala shirye-shirye da za su bayar da dammar fara shirin kashi na biyu, wanda za a gudanar a kurkukun garuruwan Zariya da Kafachan,” a cewar Lauyar gwamnati.
Shugaban Hukumar Kurkukun Jihar Kaduna, Yazid B. Alhassan, ya yaba da kokarin wadanda suka shirya shirin., wadanda suka tabbatar da samun nasarar aiwatar da shirin.
Ya ce don haka muka yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki da kafafen yada labarai da sauran al’umma da kamfanoni masu zaman kansu su tallafa wa ’yan kurkuku wajen ba su horo makamancin wannan.
Wakilin daliban da aka yaye, Mista Chinedu ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta taimaka musu ko da kudin ko kayan aiki don su fara harkokin kasuwanci a wannan fani da suka smau horo.
Ya yi kira ga kwmamishinar shari’a da ta sa gwamnan jihar ya yafe musu tunda sun gane kurensu.
dan kurkukun ya jajirce kan cewa irin wannan shirin zai tallfa wajen shawo kan aikata miyagun laifuka a cikin al’umma, tunda duk dan kurkukun da ya kamala wa’adin hukuncin da aka deba masa, ya fi son karkata akalar rayuwarsu wajen managarcin aiki gwargwadon yadda aka horar da shi, sabanin sake aikata miyagun laifuka.