✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar esep-le berger ta karrama Sarkin Hausawan Kwatano da digirin Dokt

Jami’ar Esep-Le Berge da ke Kwatano a kasar Benin ta karrama Mataimakin Shugaban Kungiyar ’Yan Najeriya (NIDO) kuma Sarkin Hausawan Kwatano, Alhaji Muhammadu Mouniru Garba…

Jami’ar Esep-Le Berge da ke Kwatano a kasar Benin ta karrama Mataimakin Shugaban Kungiyar ’Yan Najeriya (NIDO) kuma Sarkin Hausawan Kwatano, Alhaji Muhammadu Mouniru Garba Nakura da digirin girmamawa na Dokta. Wannan ne karo na farko da wata jami’ar kasar ta bayar da irin wannan kyautar girma ga Bahaushe dan Najeriya da ke zaune a kasar.

Ministar Ilimi ta Jamhuriyyar Benin, Uwargida Marie Odile Attanasso ce ta wakilci Shugaba Patrice G.

Talon a gagarumin bikin yaye dalibai 281 na shekarun 2017 da 2018 da Jami’ar ta Esep-Le Berge ta gudanar a babban zauren taro na St. Charbel.

Manyan ’yan kasuwa ’yan Najeriya, musamman Hausawa da ke zaune a kasashen Nijar da Togo da Ghana ne suka halarci wajen  bikin don taya dan uwansu murnar wannan girmamawa.

Cikin jawabinsa bayan ya mika takardar shaidar Dokta ga Sarkin Hausawan, Shugaban Jami’ar, Farfesa Germain Ganlonon ya ce kwamitin da jami’ar ta nada domin gano mutanen da suka cancanci digirin girmamawan ne ya gano cewa Dokta Mouniru Garba Nakura ya cancanci  wannan girmamawa saboda sadaukar da kai da dukiyarsa wajen taimakon al’umma.

Ya ce “Muhimmai daga cikin abubuwan taimakon jama’a da ya dade yana aiwatarwa da za su dada kawo ci gaban kasashen Benin da Najeriya da hadin kansu sun hada da daukar nauyin karatun marayu da marasa galihu daga firamare zuwa jami’a da bayar da tallafin kudi ga daliban Najeriya da ke karatu a jami’o’i daban-daban na kasar Benin da gina makarantar firamare shekara 17 da suka wuce a Unguwar Zango a birnin Kwatano, tare da gina sabuwar kasuwar zamani da mutane fiye da dubu daya suke samun abin dogaro da kai bayan Gwamnatin Benin ta kore su daga tsohuwar kasuwar dabbobi.”

Farfesa Golonon ya nemi Sarkin ya ci gaba da gudanar da irin wadannan ayyuka na taimakon jama’a kuma ya yi kira ga masu hannu da shuni su yi koyi da shi wajen amfani da dukiyarsu domin daukaka darajar ilimi a kasar Benin.

Cikin jawabisa bayan sanya masa riga da hular girmamawa da mika masa satifiket, Jakadan Zama Lafiya na Afrika, Dokta Muhammadu Mouniru Garba Nakura ya gode wa Jami’ar Esep-Le Berge da ta karrama shi a idon duniya.

Ya yi kira ga dalibai ’yan Najeriya da ke karatu a manyan makaratun kasar Benin su girmama dokokin kasar domin daukaka darajar kasarsu Najeriya a idon duniya. Kuma ya yi kira ga sauran jama’a musamman ’yan kasuwa mazauna Benin su kasance cikin hadin kai da tafiya da murya daya a kan dukan al’amuran da suka shafi rayuwarsu.

Unguwar Zango dai mazaunin Hausawan garin Kwatano ta cika makil da mutane, inda  wadansu suka yi ta kade-kade da raye-rayen gargajiya, domin nuna murna ga jagoran al’ummar Arewacin Najeriya da ke zaune a kasar Benin, saboda samun wannan digiri na girmamawa.