Cibiyar nan da ke fid da matsayin jami’o’i a duniya wato The Times Higher Education World Rankings ta ayyana jami’ar Afe Babalola da ke Jihar Ekiti a matsayin wacce ta fi kowacce a Najeriya, kuma ta 400 a duniya.
Shugaba Buhari ya taya Shugaban jami’ar da ma’aikanta murnar zamowa jami’ar da ta fi kowacce a Najeriya.
- Tukunyar gas din mai shayi ta kona mutum 23 a Lere
- EFCC na tuhumar mai kamfanin wallafa littattafai na Macmillan kan damfarar N65m
Haka zalika Buhari, a sakon taya murnar da ya fitar ta bakin kakakinsa Femi Adesina ranar Litinin, ya yaba wa tsare-tsaren jami’ar, da ya ce sune suka kai ta ga wannan matakin.
Ya kuma ce zamowa zakaran gwajin dafi daga jami’o’i 197 da ke Najeriya, da kuma kasancewa ta 400 a duniya daga cikin 31,097, ba karamar nasara ba ce ga Najeriya baki daya.
Don haka ya taya shugabanni da ma’aikatan jami’ar murna, tare da fatan za su cigaba da jajircewa a ayyukansu don kara ciyar da jami’ar gaba.