✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Bayero ta karrama Farfesa dangambo a matsayin ‘Garkuwan Adabin Hausa’

Sashen Nazarin harsunan Najeriya na Jami’ar Bayero ta Kano, ya karrama shahararren Shehun Malami, masanin Adabi, Farfesa Abdulkadir dangambo a matsayin ‘Garkuwan Adabin Hausa’ a…

Sashen Nazarin harsunan Najeriya na Jami’ar Bayero ta Kano, ya karrama shahararren Shehun Malami, masanin Adabi, Farfesa Abdulkadir dangambo a matsayin ‘Garkuwan Adabin Hausa’ a sakamakon gudunmawar da yake bayarwa a fagen bunkasa ilimi na fannin Adabi.

A yayin da yake bayyani a game da karramawar, Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, na Sashen Nazarin Harsuna na jami’ar, ya bayyana cewa gudunmawar da Farfesa dangambo ya bayar a tsawon shekaru 40, ba za ta lissafu ba, a fagen yada ilimi da bunkasa shi da wayar da kan jama’ a a kan muhimmancin Adabi.
Ya ce: “Duk da cewa Malam ya yi ritaya, sannan ya nemi izinin ci gaba da bayar da gudunmawa kuma Jami’a ta ba shi wannan damar, wannan ya nuna jajircewarsa da rashin gazawarsa, duk da yawan shekarun da yake da shi.” Ya ce ya kasance sannan ne ga jama’ar gari, a sakamakon shirin Rediyo da yake gabatarwa na ilmantar da jama’a game da Adabi.
Shi ma shugaban kwamitin shirin karrama farfesan, Dokta Ibrahim Garba Satatima, ya ce masana sun gabatar da kasidu da aka hada babban kundi, wanda za a gabatar da shi, a matsayin karramawa ga Farfesa dangambo.
Ya ce: “Mun buga littafin karrama shi ne, domin mu girmama shi da abin da aka san shi a kansa, wato ilimi, saboda da zarar an gan shi, an ga ilimi.” Haka nan ya bayyana farfesan a matsayin uba kuma kaka na ’yan boko, manazarta Adabi, wanda ya ce ya yaye manyan dalibai da su ma suka zama shehunnan malamai a halin yanzu.