✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Ahmadu Bello ce jagorar habaka ayyukan noma a Najeriya – Ministan Gona

Minista a Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara, Sanata Heinken Lokpobiri ya bayyana fannin ayyukan gona da ke Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a…

Minista a Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara, Sanata Heinken Lokpobiri ya bayyana fannin ayyukan gona da ke Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a matsayin jagorar habaka aikin gona a Najeriya.

Ministan ya bayyana haka ne a ya yin ziyarar aikin gani da ido na kwanaki biyu, tare da duba irin kayayyakin da cibiyoyin aikin gonar ke da su, da kuma samar da kayayyakin irin na zamani dan habbaka binciken gwamnatin tarayya a cigaba da kakarin wadata kasa da abinci.

Sanata Heineken ya kuma bayyana kwazon da ma’aikatan musamman masu bincike da kuma na kimiyya ke nunawa ta wajen samar da ingatattun bincike dan ci gaban kasa ta fannin aikin gona da cewa abin alfahari ne, kuma ya kamata a ba su gudumuwar da ta kamata.

Ministan wanda ya tabbatar wa da cibiyoyin cewa zai tabbatar da ganin an ba su kudaden su akan lokaci domin ci gaba da aikace-aikacen da suke yi don ci gaban kasa. Ya kuma shawarci cibiyoyin da su tallata hajarsu ga al’umma tare da yin hadin gwiwa da kamfanoni don samun kudaden shiga wadda hakan zai rage yawan dogaro da gwamnati don samar da kudaden bincike. Saboda haka sai Ministan ya bayyana Jami’ar Ahmadu Bello da cewa ta kasance a bisa muhimmin matsayi ba ma a Najeriya ba, har ma da Nahiyar Afirka  baki daya.

Tun da farko a jawabinsa Shugaban Rukunin Sassan Fannonin Aikin Gona, Farfesa Ibrahim U Abubakar ya sanar da Ministan irin cigaban da suke samu tare da hadin kai da ke wanzuwa a tsakaninsu. Daga nan sai kuma Farfesa Abubakar ya roki Ministan da ya taimaka wa cibiyoyin ta hanyar sakin kudadensu akan lokaci dan ci gaban binciken.