✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’ar ABU za ta fara musayar ilimin aikin gona da takwararta a Ingila

Aliyu Babankarfi Zariya Jami’ar Ahmadu  Bello (ABU), Zaria ta ƙula yarjejeniya da jammi’ar Yammacin Scotland domin bunƙasa amfanin gona a nahiyar Afrika. Daraktan yaɗa labaran…

Aliyu Babankarfi Zariya

Jami’ar Ahmadu  Bello (ABU), Zaria ta ƙula yarjejeniya da jammi’ar Yammacin Scotland domin bunƙasa amfanin gona a nahiyar Afrika.

Daraktan yaɗa labaran ABU Malam Auwal Umar ya ce an ƙulla yarjejeniyar ne ƙarƙashin shirin Musayar Ilimin Noma na Nahiyar Afirka.

An koma karatu a Jami’ar Ahmadu Bello

Jami’ar Ahmadu Bello ta kirkiro sabon takin zamani don bunkasa noma

Yace ƙawancen zai taimaka wurin musanyar ilimi kan dabarun bunƙasa ribar ƙananan manoma da kamfanonin sarrafa amfanin gona a ƙasashen Nigeria, Ghana, Kenya da Afirka ta Kudu.

Malam Auwal Umar yace Ƙungiyar ƴan Afirka mazauna Scotland ce ta taimaka wurin ƙulla alaƙa tsakanin jami’o’in biyu.