Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta sanar da naɗa sabon shugabanta, Farfesa Adamu Ahmed.
Majalisar Gudanarwar jami’ar ce ta zaɓi Farfesa Adamu Ahmed a matsayin wanda zai maye gurbin Farfesa Kabir Bala.
An sanar da zaɓen Farfesa Adamu da misalin ƙarfe 6:15 na safiyar wannan Larabar a yayin zaman Majalisar Gudanarwar jami’ar wanda Mahmud Yayale Ahmed CFR ya jagoranta.
Farfesa Adamu Ahmed dai malami ne a sashen nazarin tsara birane na jami’ar ta ABU.
Ya taɓa riƙe muƙamin Darektan Cibiyar Bunƙasa Jami’ar kuma a yanzu shi ne Uban Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Kano.