✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an zabe sun yi bore a Kano

Ma'aikatan zabe sun yi barazanar kaurace wa aikin ana tsaka da rabon kayan aikin zaben shugaban kasa a safiyar Asabar

Ma’aikatan zabe sun yi bore tare da da barazanar kaurace wa aikin, a unguwar Dorayi Karama da ke Karamar Hukuma Gwale a Jihar Kano.

Ma’aikatan zabe na wucin gadi sun yi barazanar ce a lokacin da ake tsaka da rabon kayan aikin zaben shugaban kasa da ’yan Majalisar Tarayya a safiyar Asabar.

Boren nasu ya samo asali ne da zargin da suke yi cewa an yi musu kwange wajen biyan su kudin alawus dinsu na samun horo.

A kan haka ne suka yi yunkurin hana ci gaba da rabon kayan aiki sannan suka jadda cewa ba za su yi aikin ba, sai an cika musu kudin alawsu dinsu.

A cewarsau, suna samun da labarin cewa N7,000 aka biya takwarorinsu a wasu jihohin, amma su N3,000 aka ba su.