✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaron Amurka sun harbe mutumin da ya yi barazanar kashe Joe Biden

Jami’an tsaron Amurka sun harbe mutumin da ya yi barazanar kashe Joe Biden

Jami’an Hukumar Binciken Tsaro ta Amurka (FBI), sun hallaka wani mutum da ya yi barazanar kashe Shugaban Kasar, Joe Biden.

Kafar yada labarai ta BBC ta rawaito cewa jami’an sun kashe mutumin ne mai suna Craig Robertson a Provo, mai nisan kilomita 65 kudu da birnin Salt Lake da ke Utah.

Rahotanni sun ce an kashe shi ne duk da ana gudanar da bincike a kan shi, wanda aka fara a watan Afrilun da ya gabata.

Ana zargin mutumin ne da wallafa wani sako da ya wallafa yana barazanar kashe Biden din idan ya ziyarci yankinsu.

Kakakin FBI ya ce, “Lamarin ya faru ne lokacin da jam’ianmu na musamman suka yi yunkurin shiga gidansa su ba shi takardar izinin kama shi da kuma caje gidansa.

“Yanzu haka mutumin ya kwanta dama. Mu ba ma daukar kowacce irin barazanar kisa da wasa.”

Jami’an dai na shirin kai wa mutumin takardar sammaci ne ga Roberstson, ’yan sa’o’i gabanin ziyarar da aka shirya Biden zai kai jihar sa.