Al’ummar karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto sun tabbatar da cewa jami’an tsaro a yankin sun kara matsa kaimi wajen sintiri bayan da harin ‘yan bindiga ya yi sanadiyyar kisan sama da mutane 74 a makon jiya.
“Yanzu haka akwai dimbin jami’an ‘yan sanda da na sojoji da ke ta karakaina a yankunanmu”, in ji wani mazaunin yankin.
A cewar wani mazaunin yankin shi ma, “Jami’an tsaron na yin sintiri a kauyukan Garki da Dan Aduwa inda akasarin mazauna kauyukan suka yi gudun hijira zuwa garin Sabon Birni.
Mazauna yankunan sun yi kira ga hukumomi da su karasa fatattakar ragowar ‘yan bindiga daga dazukan dake kewayen yankunan nasu, suna masu cewa wuraren masu laifin ke amfani da su a matsayin mafaka.
- Za a tallawafa wa wadanda harin Sokoto ya rutsa da su
- An kashe mutum 70 a Sabon Birni bayan ziyarar gwamna Tambuwal
Wakilinmu ya rawaito cewa akasarin mazauna kauyukan yanzu na zaune ne a makarantar firamaren gwamnati ta garin na Sabon Birni, yayin da wasu kuma suka samu mafaka a gidajen ‘yan uwansu a wasu garuruwan.
A cewar mazauna garin na Sabon Birni, akwai sama da mutane 100 daga kauyukan Garki da Dan Aduwa, yawancinsu mata da kananan yara, a garin.
Kwana a tshar mota
Sun kara da cewa wasu daga cikin ‘yan kauyukan sun rika kwana a tashoshin mota kafin su karaso garin.
A wani labarin kuma, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya koka da yawan hare-haren ‘yan bindiga da sauran kalubalen tsaro da ke haddasa rasa rayukan mutane a kasa.
Ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin Babban Hafsan Sojojin Sama na Najeriya a fadarsa, lokacin da Air Marshall Sadique Abubakar ya kai ziyara don duba barnar da harin da ‘yan bindiga suka yi a Sabon Birni.
Sarkin Musulmin ya kara da cewa akwai bukatar kara samar wa da jami’an tsaro karin kudaden gudanarwa, yana mai Allah-wadai da harin da ya hallaka akalla mutane 74 a ‘yan kwanakin nan.
Da yake jawabi tun da farko, Sadique Abubakar ya ce ya je Sakkwaton ne don duba girman barnar da harin ya yi da nufin gano bakin zaren, kamar yadda Shugaba Buhari ya bayar da umarni na yin luguden wuta kan ‘yan bindigar.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal, ya ziyarci fadar shugaban kasa don tattauna kalubalen tsaron jihar.
Ya ce jihohin Arewa Maso Yamma da jihar Naija da ke Arewa ta tsakiya za su hada karfi da karfe don magance matsalar tsaron da ta addabi yankunansu.