Jami’an ’yan sanda da na Sibil Difens sun hana magoya bayan jam’iyyar NNPP da suka taru a filin Mahaha da ke Kano don yin sallar neman nasara ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Aminiya ta rawaito cewa an fuskanci hatsaniya jim kaɗan da kammala irin wannan addu’ar a ranar Laraba, inda mutane suka yi taho-mu-gama da ’yan sanda.
- Boko Haram Ta Ba Mazauna Yankunan Borno 8 Kwanaki 3 Su Tashi
- Kotun Daukaka Kara ta tabbatar wa APC kujerar Gwamnan Nasarawa
Dubban mutanen dai sun fantsama kan titunan Kano suna neman kotun ɗaukaka ƙara ta yi wa Abba adalci bayan kundin shari’ar da ta fitar ya nuna bayanai masu cin karo da juna, inda a wani shafin ya nuna shi ma ya yi masara a shari’ar.
To sai dai lokacin da mutanen suka sake taruwa a filin na Mahaha da ke Ƙofar Na’isa, sun ci karo da jami’an na NSCDC, waɗanda suka hana su shiga filin.
An dai tsara yin sallar ne da misalin karfe 10:00 na safe, amma sai aka ɓige da yin kallon-kallo tsakaninsu da jami’an tsaron, kuma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba a bar su sun yi sallar ba.
Mutanen dai sun yi cirko-cirko a Daura da filin, yayin da su kuma jami’an tsaron suka yi wa filin ƙawanya suka hana a shiga ciki.
Sai dai duk ƙoƙarin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Amma Kakakin NSCDC a Kano, DSC Idris Abdullahi, ya shaida wa wakilin namu cewa an girke jami’an ne saboda a tabbatar mutane ba su yi amfani da yanayin wajen karya doka a Jihar ba.