✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jama’a na tserewa daga garinsu saboda janye sojoji a Neja

Daruruwan mutane sun bar kauyukansu bayan sun wayi garin Alhamis da ganin an rufe sansanin sojojin da ke yankin karamar hukumar Shiroro

Jama’a sun yi hijira bayan an rufe sansanin soji da kuma janye sojoji da ake aikin samar da tsaro a kauyen Allawa da ke Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

A ranar Alhamis ne sojojin Najeriya suka rufe sansaninsu, wanda ya janyo firgici a tsakanin al’ummar yankin da ke fama da hare-haren ’yan bindiga da mayakan kungiyar Boko Haram da ISWAP.

Allawa dai na daya daga cikin al’ummomin da ke fama da munanan hare-hare ’yan ta’adda a karamar hukumar Shiroro.

Mazauna yankin sun ce j anye sojojin ya zo musu da mamaki saboda a yanzu haka su d makwabtansu na fama da sabbin hare-hare.

Wannan ya sa daruruwansu, mata da tsoffi da kananan yara ficewa daga kauyen babu shiri, inda suka tasam ma tafiyar akalla kilomita 50 don neman wuraren fakewa masu aminci.

Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa sun wayi garin Alhamis ne kwatsam suka ga sojojin na kwashe tantunansu suna shirin barin yankin.

Daya daga cikinsu, da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa, janyewar ta zo ne kwanaki biyu bayan motar sojoji ta taka nakiya a kan hanyar Allawa zuwa Pandogari, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da ba a bayyana adadinsu ba.

“A ranar Talata 23 ga watan Afrilun 2024, sojojinmu da ke kan hanyarsu ta zuwa Allawa sun taka bama-bamai da suka yi sanadin mutuwar mutane, wasunsu na kwance a asibiti, lamarin ya faru ne a garin Allawa, akan hanyar Pandogari,” in ji shi.

Lamarin na ranar Talata ya zo ne kasa da mako guda bayan wasu sojoji shida da wani dan banga sun rasa rayukansu a wani harin kwanton bauna da ’yan ta’adda suka kai garin Roro.

Wannan ya faru ne a lokacin da ’yan bindiga suke kai hare-hare a garuruwan Roro da Karaga da Rumace da wasu yankuna da ake noma sosai.

Wani mazaunin garin, Malam Yahuza Allawa, ya ce, tun da misalin karfe 4 na asuba wasu da dama suka fice daga kauyen, suka nufi Erena, Gwada, wasu kuma sun nufi Kuta ko Zumba domin tsira da rayukansu.

“Wannan babban lamari ne, don Allah a taimaka mana a buga rahoto, yanzu muna kan hanyar barin garinmu, kuma babu isassun babura da motoci da za su fitar da mu cikin gaggawa.

“Muna fata watakila idan kun kai rahoto gwamnati ta kawo motocin da za su kwashe mu zuwa wasu wurare da ke da aminci, kayanmu suna can, ba za mu iya kwashewa ba.

“Wallahi daruruwan ‘yan garinmu sun riga sun bar yankin, ba za mu iya bin hanyar Pandogari ba, saboda babu tsaro, don haka za mu bi ko dai Erena ko ta Gwada ko kuma ta Kuta ko Zumba.

“Daga Allawa zuwa Erena wadda ita ce hanyar da za a iya fita daya tilo. Akalla za ta kai kilomita 42, muna takawa ne a kafa saboda babu abin hawa da zai kai mu. Akwai Boko Haram a sauran hanyoyin.”

Ya ce, manoman da ke gudun hijira na da daruruwan awaki da sauran dabbobi a gida, da ma wasu kayayyaki masu daraja da suka hada da kayan abinci da suka kasa kwashewa saboda rashin abin hawa.

Ya ce Allawa da al’ummomin da ke makwabtaka da su sun dogara ne da kasancewar sojoji domin kariya, wanda janye su ya zo musu da mamaki.