Kimanin wata shida bayan aika jakadan Isra’ila zuwa kasar Morocco, har yanzu kwana da aiki daga otel inda yake fadi tashin samun inda zai tsugunar da ofishin jakadancin.
A watan Janairu ne aka nada David Govrin a matsayin jakadan Isra’ila a kasar Morocco bayan da hukumomin Rabat suka dawo da huldar diflomasiyya da Isra’ila a bara, inda ta zama kasar Larabawa ta hudu da ta yi hakan cikin shekara biyu.
- Yadda Fani-Kayode ya hada ni da Nnamdi Kanu — Asari Dokubo
- Za mu kwato dubban kadarorin Hukumar Gidan Waya — Pantami
A cewar rahotannin da ke fitowa daga dukkanin kasashen biyu, masu gidajen haya a Rabat, babban birnin Morocco sun ki ba da hayar gidajensu domin tsugunar da ofishin jakadancin Isra’ilar.
“Kamfanin da aka bai wa jingar nemo matsugunin ya samo wani gidan da ya dace a wata unguwar masu hali a birnin Rabat, wanda jakada Govrin ya amince da gidan ya cika sharuddan tsaron da ake bukata,” kamar yadda wata jaridar kasar da ake wallafa wa a intanet mai suna Assahifa ta fitar a makon jiya.
“Sai dai kash! Inda matsalar take, da suka gano ko wane ne mai neman hayar, masu gidan ba tare da wata inda-inda ba sun ki ba da hayar gidansu ga jami’in diflomasiyyar Isra’ilar.”
Jaridar ta ruwaito wata majiya a kasar tana cewa irin hakan ya faru “a wasu gidajen da ke unguwar.”
Wannan lamarin ya sanya Mista Govrin, wanda tsohon jakadan Isra’ila ne a kasar Masar, har yanzu yana zama a wani otel a birnin na Rabat, a cewar jaridar.
Sanarwar dawo da huldar diflomasiyyar da kasar Morocco ta yi da Isra’ilar a watan Disamban bara ta haddasa zanga-zanga da dama a kasar domin nuna kin jinin matakin.