Shugabar kungiyar Mata ta kasa (NCWS), reshen Jihar Yobe Hajiya Halima Joda, ta ce tashi tsayen da suka yi kan masu fyade ne ya sa gwamnatin Yobe yin dokar daurin rai-da-rai ga masu yi wa kananan yara fyade a jihar.
Hajiya Halima Joda, ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da Aminiya inda ta ce bala’in yi wa kananan yara fyade a Jihar Yobe ya zama annoba su kuma kasancewarsu iyaye suke ganin bai kamata a bari ba a dauki doka a kan masu yi ba.
Ta ce abin takaici shi ne sai ka ga tsoho dan shekara 70 zuwa 80 yana daukar yara kanana da ba su wuce ’ya’yan jikokinsa ba masu shekara bakwai wani lokacin ma ’yan watanni da haihuwa suna yi musu fyade.
Shugabar ta kara da yin kira ga iyaye cewa ba fata ake yi ba, amma duk uwa ko uban da aka yi wa ’yarsa fyade kada su boye su fito su fada don bi musu hakkinsu na kamo wanda ya aikata don gurfanar da shi a gaban shari’a.
Hajiya Halima Joda, ta ce gaskiya a Jihar Yobe idan da ba domin wannan doka da aka bullo da ita ba na tsoron dauri da ba a san ko za a samu sauki na wannan annobar fyade ba.
Sai ta gode wa ’yan Majalisar Dokoki ta Jihar Yobe kan yadda suka amince da bukatar Gwamnan wajen sanya hannu a dokar da aka bullo da ita na daurin rai-da-rai ga duk wanda aka kama da yi wa kananan yara fyade ko dan wane ne.