✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jahilci

Wani mutum ne yana zaune da matarsa mai suna Hamida a gida, kullum idan ta yi masa laifi sai ya rika cewa zai sake ta,…

Wani mutum ne yana zaune da matarsa mai suna Hamida a gida, kullum idan ta yi masa laifi sai ya rika cewa zai sake ta, sai wata rana da ya gaya mata cewa zai sake ta sai ta ce masa: “Maigida kana saki na shi ke nan sai in je in auri limamin garin nan.” Da jin haka sai maigidan ya zaro ido ya ce: “To da ma ashe liman son ki yake, shi ya sa idan yana Sallah yake cewa ‘sami Allahu liman Hamida?”
Daga Rabilu Abubakar Gombe, 08036597674