Hukumar Kwallon Kafar Turai UEFA, ta fitar da sabon jadawalin gasar cin Kofin Zakarun Turai na kakar wasanni ta 2021/2022.
A yayin bikin fitar da jadawalin da aka gudanar ranar Alhamis a birnin Istanbul na kasar Taki, UEFA ta ce wasannin gasar za su fara daga 14 ga watan satumba mai kamawa zuwa ranar 28 watan Mayun 2022.
- Bam ya tashi a kusa da filin jirgin sama na Kabul
- Tattalin arzikin Najeriya ya karu a rubu’i na biyu na 2021 —NBS
A rukunin farko na jadawalin wato rukunin A, ya kunshi kungiyoyin kwallon kafa 4 da suka hada da Man City da PSG da RB Leipzig da kuma Club Brugge.
A rukunin B kuwa akwai Atletico Madrid da Liverpool da Porto da kuma AC Milan.
Sai rukunin C da ya kunshi Sporting da Borussia Dortmund da Ajax da kuma Besiktas.
Akwai kuma rukunin D da ya kunshiInter, Real Madrid, Shakhtar Donetsk da kuma Sheriff Tiraspol.
Sai rukunin E da ya kunshi Bayern Munich da Barcelona da Benfica da kuma Dynamo Kyiv.
Akwai kuma rukunin F da hadar da Villarreal da Manchester United da Atalanta da kuma Young Boys.
Sai rukunin G da ya kunshi Lille da Sevilla da Red Bull Salzburg da kuma Wolfsburg.
Kana rukunin H kuma na karshe da ya kunshi Chelsea, Juventus, Zenit St Petersburg da kuma Malmo.
Ga jadawalin a takaice
Group A: Man City, PSG, RB Leipzig, Club Brugge
Group B: Atletico Madrid, Liverpool, Porto, AC Milan
Group C: Sporting, Borussia Dortmund, Ajax, Besiktas
Group D: Inter, Real Madrid, Shakhtar Donetsk, Sheriff Tiraspol
Group E: Bayern Munich, Barcelona, Benfica, Dynamo Kyiv
Group F: Villarreal, Manchester United, Atalanta, Young Boys
Group G: Lille, Sevilla, Red Bull Salzburg, Wolfsburg
Group H: Chelsea, Juventus, Zenit St Petersburg, Malmo