Jan-janin janye wuri
dan kwadago da na-mujiya wuri-wuri
Matsaloli sun sa an yi kuri
Jiki na hajijiyar jin jiri
Ko kwanyara kukan jinjiri
Dankari makari
Da hunturu an fito firi-firi
Kar ku ganni a firgigi
Haurobiyawa ban da walagigi
Lallai za a kwance mana sasari
Baba yai mana tari
Na dan yi mura da tari
Mai ingarma ba ya hawa kuturi
Miyagu sun sa a na jan kari
Ta’asa sai an kaita kabari
Jayayyar juyin shekara
Jan-ragamar mai fikira
Fuffukar-fuka-fukin fakara
Farantin taliyar cin tara
Fafutikar takarar taka-kara
Jan dagar jarumi
Na-raye da na-mujiya yai arba
Nagartar mutum mutu ka raba
Jinkirin rabon mukami
Rudanin masu bambami
Dubun karamin laujen silin magirbi
Baba ya zare takobi
Zai sauke kurungun ayyukan aibi
Mu dai mu yi dabgen zabi
A hada mana kulorar jangahur da zabibi
Gayauna za ni da masassabi
Tuni na warware daga zazzabi
Na daina jin zafi a kwibi
Ku taho kowa ya bi
Garkar gayauna labi-labi
Giringidimin gangarowar Girigogriya
Gagarumar shekara
Gagara-kuwar ’ya’yan asara
Gagarabadau daura aniya
Gurguri goribar gwagwarmaya
Tattalin tulin dukiya
Mai na-duke da kiwon tunkiya
Gayauna tai yabanya
Uwargida sanye da abaya
Na ga maigida da jallabiya
Ai wa kasa sutura takamala
Aikin ingata ra yuwa ya malala
Gayauwna mun bar wasu na ta kala
Mui watsi da masu takala
Makirai an tsala musu bulala
Tun farkon Hijiriya
Kyawawan dabi’u ake ta bibiya
Ha mu a sabuwar Girigoriya
Gasuwar Baban-buron-huriyya
A daina duk wata dirkaniya
’Yan kasa za su yi dariya
Garar dabgen dadin duniya
Girkin ga hada da tsuntsun miya
A damo kunun tsamiya
Gasarar koko a kwatanniya
A kandamo gudajin gaya
Jalli-jogar janjalo
Hallo alalo
Sidddabarun dabara salo-salo
Ka shige cikin gwalalo
Ka yi wa jama’a gwalo
Bayan kowace wahala
Da ta haifar da lalala
Jikin wasu yai kasala
Har wasu sun hassala
Da hutu sai a taba dafdala
Gargadin gudun gara
In an fada zago an makara
A zo ana neman kakara
Al’umma a daina kagara
Mu kara kaimi kowa ya zabura
Farko zuwa karshen shekara
An samu dimbin al’amura
Wasu sun faskara
Bara-gurbi sun yi wasan dara
Da walwalin waliyon mashillara
Ja-in-jar Janye-wuri
Fankamar Farin-biri
Marisar marmari
A-farin-lilon wata nagari
Mayun-miyagu a garari
Yawon-wuni
Yawon-wulli
Agusata na ruwan tulu tuli
Sautun-tumun-Baba babu balli
Ukkun-toton Baba mai iyali
A zo Noman-Baba
karshe dai Dashen-Baba
Ai ta sakar tabarmar kaba
A kiyayi jagaliyar ’yan daba
A kiwo an kora ’ya’yan dabba
Tabbacin rashin tababa
Haurobiyawa a daina gaba
A kiyayi giba
Mu hau bisa kyakkyawar turba
A girgoriya mu kara samun tsaba
Sabanin yadda haurobiyawa suka saba yi wa juna fatan alheri da adu’o’i nagari duk sa’adda aka NAUYAYYA-NIYYAR sabuwar shekara ta HIJIRIYYA ko GIRIGORRIYA, wannan karo sai aka karke da JA-IN-JAR JANYE-WURI da JAN-JANIN-JAN-NA-MUJIYA yai kURI, wai saboda Baban-burin-huriyya ya bai wa matattu mukami. Wannan lamari ai ta kwana gidan sauki, domin faduwar wani tashin wani, sai a daina duk wani wuni-wuni.
Mu kauce wa kwaramniya, musamman masu neman kamuya-muya a sabuwar shekarar Girigoriya, don ya zama dole mu gwagwiyi goribar gwagwarmaya, don kada a yi mana mamaya. Farkon wata dai ya tsaya.
Baba dan Adam ne na san yana kuskure, amma bai cika yin ganganci ba, musamman kan al’amarin da ya shafi jan ragamar al’ummar kasa, tunda ai yana so kowa ya warwasa, mu ci WASA-WASA. Kuma ko a farfajiyar wannan katafariyar makaranta mun sha bijiro muku da batun yadda za a kwashi KWALAM da MAkWALASHE, mu ce wa miyagu CIN-BIM-kWALAM!
Batu na ingarman karfen karafa, muna fatan ganin Baba ya samu galaba a kan masu karfa-karfa da suke yi mana fafa, wadanda aikinsu ya zafafa, musamman yadda a dukan ta-mola suke fafutikar ganin sun zarta FIFA!
Baba kura ta lafa, amma kada a yi wasararai da tsillin matsala kodabata wuce kan akaifa ba. Ba za mu lamunce da kowace kutungwila da ke sanya al’umma ta hassala ba. Mu yi hadakar hadin gwiwar karfen karafan kwangiri titin taragon dogo a daukacin lokacin wulwulawar agogo ta yadda za mu tuinkari mai kilago mu tamke shi da da bawon kalgo, Baba ne dai babban jigo wannan balaguro don haka na raba muku marsa goriyar goro. Kow aya samu hoto ku zo mu yi taro, ta yadda in jinbirin wake ya nuna babu wanda zai kasala a wajenm roro.lallai mun JIMIRI DA JINKIRIN CIN JINbIRI!
Ni dai shawarata Baba da sauran managarta mutanen da ke jan-ragamar al’umma lallai su daina kula jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, domin ba su da wani katabus, tunda an kawo karshen camamar cin cammas da cin CUKUBUS su yi ta tusa tus-tus!
Baba da Inna lallai a dauki tsintsiya a share mana jiba da daukacin kazantar tsilli-tsillin matsalolin da suka dabaibaye Haurobiya, ta yadda kowa sai ya yi dariya, sannnan mu himmatu ka’in da na’in wajen kyautata tunani da agaza wa juna. Mu yi kishin kasa ban da KISSA da KISISINAR KISHIYA, al’amarin da ke haifar mana jibga wa juna JIbAR TSIYATAKU, Haurobiyawa Gwamnati ta sauya managarcin SALON KIdA lallai sai mu sauya TAKU!