Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa da ke Jos, ta bukaci Majalisar Dattawa da ta Wakilai su sa baki a kan yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), take yi a kasar nan, don ganin an kawo karshen wannan matsala.
Kungiyar ta bayyana wannan bukata ce a wajen rufe taron kara wa juna sani na kasa na kwana uku karo na 29, da ta shirya a garin Jos.
Da yake bayyana wannan bukata, Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa ta Kungiyar, Sheikh Muhammed Sani Yahya Jingir, ya ce, “A matsayinmu na ’yan Najeriya da muka zabi wadannan ’yan majalisa, ya zama wajibi su fito su sa baki, domin malaman jami’o’i su janye wannan yajin aiki da suke yi.”
Ya ce bai kamata ’yan Majalisar Dattawa da ’yan Majalisar Wakilai su yi shiru kan wannan matsala ba, musamman idan aka dubi mawuyacin halin da dalibai da iyaye suke ciki.
“Talakawa ne suke shan wahala, kan wannan yajin aiki. An ware sama da Naira biliyan uku don dauko daliban Najeriya daga Ukraine.
“In har gwamnati za ta ware wadannan kudade don dauko daliban daga waje, ya kamata ta biya wa malaman jami’o’i bukatunsu, don su janye yajin aikin da suke yi,” inji shi.
Sheikh Jingir ya ce ya kamata shugabanni su san cewa kafin su kai ga matsayin da suke kai, sai da malaman jami’o’in suka karantar da su.
“Su ma malaman jami’o’in nan ya kamata su tausaya wa dalibai da iyayensu, su koma bakin aiki, domin su ne suke shan wahala kan wannan yajin aiki,” inji shi.
Ya ce “Gwamnati ku daidaita da malaman jami’o’in nan, domin mun matsu ’ya’yanmu su yi karatu.
“Wadansu jami’an gwamnati sun dauki ’ya’yansu sun kai kasashen waje karatu. Don haka ’ya’yan talakawa ne suke shan wahalar wannan yajin aiki.”
Taron kara wa juna sani na kwana uku da kungiyar ta shirya, ya samu mahalarta daga dukkan jihohin Najeriya da kasashen makwabta.