✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyayena daga Sakkwato da Jigawa suke – Atiku

Dantakar Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya ce iyayensa asalinsu ’yan Arewa maso Yammacin Najeriya ne don haka yana da ’yancin da zai tsaya takarar shugabancin…

Dantakar Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya ce iyayensa asalinsu ’yan Arewa maso Yammacin Najeriya ne don haka yana da ’yancin da zai tsaya takarar shugabancin Najeriya.

Atiku da Jam’iyar PDP suna mayar da martani ne ga Jam’iyyar APC, wadda ta bayyana wa Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Shugaban Kasa ran 18 ga Afrilu cewa Atiku ba dan Najeriya ba ne.

Jam’iyyar APC ta yi zargin cewa Atiku dan asalin kasar Kamaru ne don haka bai cancanta ya rike ofishin Shugaban Najeriya ba kamar yadda tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya bayyana.

Jam’iyyar ta ce garin Jada da ke Jihar Adamawa da aka haifi Atiku a ranar 25 ga watan Nuwamba 1946, a wancan lokaci yana karkashin kasar Jamus ce, bayan Yakin Duniya na farko da aka yi nasara a kan Jamus a 1918 sai ikon yankin ya dawo karkashin Majalisar Dinkin Duniya, daga bisani yankin na Adamawa ya dawo Najeriya a bayan ’yancin kai da shekara daya a 1961.

A takadar da lauyoyinsa suka gabatar sun yi bayani cewa mahaifin Atiku mai suna Garba Atiku Abdulkadir dan asalin Najeriya ne ta hanyar haihuwa wanda ya fito daga Jihar Sakkwato, mahaifiyar Atiku kuma ta fito ne daga Jihar Jigawa. Kuma ’yan asalin Najeriya ne kuma daga kabilar Fulani.

“Dangane da haihuwar Atiku a Jada, ya faru ne saboda hijirar da kakan Atiku ya yi daga Wurno a Jihar Sakkwato zuwa Jada da ke Jihar Adamawa saboda fatauci tare da abokinsa Ardo Usman.’’

Atiku ya yi aiki a Hukumar Kwastam, sannan ya yi takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar SDP a 1992 sannan ya zama Mataimakin Shugaban Najeriya har sau biyu daga 1999 zuwa 2007.

Atiku ya mayar da martani ga lauyoyin APC cewa ba su da kwarewa domin ba su yi la’akari da dokar da aka samar a shekarar 2017 ba, wacce ta yi bayani a kan ’yan kasa.