✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Iyalan ma’aikatan da suka rasu sun shirya addu’a ta musamman don neman hakkokinsu

Tsoffin ma'aikatan Gwamnatin Filato na bin ta bashin hakkokinsu na Naira biliyan takwas

Iyalan ma’aikatan Gwamnatin Jihar Filao da suka rasu sun shirya addu’o’i na musamman domin gwamnatin ta biya su hakkokinsu da suka makale.

Guda daga cikin iyalan wadanda suka rasun, Bryana Luka, ya ce yawancin iyalan ba a biya su ko kobo ba tsawon shekaru, shi ne suka shirya addu’ar ta kwanaki uku domin neman agajin Ubangiji kan mawuyacin halin da suke ciki.

“Da yawa daga cikinmu sun dade suna bibiyar hakkokin nan na tsawon lokaci.

“Don haka muka shirya addu’ar nan da zummar jan hankalin gwamnanmu da shugaban ma’aikata, hadi da Majlisar jiharmu su tausaya mana.

“Mun sha wahala, kuma da dama daga cikinmu sun rasu suna kan bibiyar hakkokinsu,” in ji shi.

A nasa bangaren, Shugaban Ma’aikatan jihar, Sunday Hyat, ya roki iyalan mamatan da su kara hakuri, domin gwamnati  na yin iya kokarinta wajen magance matsalolin da suka shafi biyan hakkokin nasu.

A cewarsa, gwamnati mai ci ta gaji bashin kudin fanshon ma’ikata tun daga lokacin mulkin soji da na farar hula, wanda ya sanya abin ya yi mata yawa.

“A lokacin da wannan gwamnati ta zo, bashin da ke kanta ya haura na Naira biliyan takwas.

“Bashin ya hada da biliyan N2 na garatuti, biliyan N3 na fansho, sai kuma biliyan N3 na wadanda suka rasu.”

Hyat ya bayyana cewa gwamnatin ta fara biyan kudaden fansho, amma karancin kudi ya kawo mata kalubale, amma da zarar ta kammala tattara kudade, za ta sallame su.