✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Iyalan fasinjojin jirgin kasan Kaduna za su tare a ofisoshin gwamnati

Sun bayyana fargabar kan samun labarin rashin maganin sarar maciji da na harbin bindiga da ’yan uwansu ke fama da su a hannun ’yan bindiga.

Iyalan sauran fasinjoji 50 da har yanzu suke hannun ’yan bindigar da suka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun yi barazanar tarewa a gine-ginen gwamnati a Kaduna da Abuja, muddin ba a kwato musu ’yan uwa ba.

Sun kuma bayyana fargabar da suka shiga sakamakon samun labarin rashin maganin sarar maciji da na harbin bindiga da ’yan uwan nasu suke fama da su a hannun ’yan bindiga.

Dokta Abdulaziz Atta, wanda aka sace wa ’yar uwa da mahaifiya, ya ce yana cikin tsananin damuwa kan halin da lafiyarsu take ciki yanzu haka.

Ya ce: “A jaridu muka karanta yadda aka harbi dan uwanmu Al’amin da ke hannun ’yan ta’adda sakamakon kuskuren guda daga masu gadinsu.

“Amma abin tambaya shi ne a wane hali sauran suke ciki yanzu? Musamman ganin babu magani, babu mai cire harsahin daga jikinsa, ga shi kuma a tsakiyar daji, yana bukatar taimako, idan bai samu ba mutuwa zai yi.”

Ya cigaba da cewa: Dduk da mun san gwamnati na kokari, tunda har an sako 11 daga ciki, amma akwai bukatar kara kaimi domin duk kwanan da fasinjojin ke karawa a hannun ’yan ta’adda hadari ne ga rayuwarsu.

“Don haka ina kira ga wakilan gwamnati da ke jagorantar tattaunawa da ’yan bindigar, ya kamata su kara kaimi su ma — Mu abin da kawai muke so shi ne a sako ’yan uwanmu.

“Muna da kananan yara da ba su fi shekara uku ba a cikin wadanda aka sace kuma ba a ba su kulawa, ga mata masu rauni da tsofaffi; Ya kamata su taimaka mana”, in ji shi.