’Yan ta’addan ISWAP da suka yi garkuwa da wani ma’aikacin kiwon lafiya a Jihar Borno, Bulama Gaidam, kimanin watanni 11 da suka gabata a yanzu, sun sake shi.
Rahotanni sun ce ’yan ta’addan sun saki Bulama ne a garin Gubio, daga bisani kuma aka wuce da shi zuwa birnin Maiduguri domin mika shi ga iyalansa.
- Tsoffin kudi: Jihohi 12 sun nemi Kotun Koli ta soke umarnin Buhari
- Canjin kudi: Dalilin da Tinubu ke tausaya wa talakawan Najeriya
To sai dai kuma babu cikakken bayani ba kan ko an biya kudin fansa kafin a sako shi, ko kuma a’a.
Tun a cikin watan Maris din 2022 ne ’yan ta’addan suka kame Bulama lokacin da suka kai wani farmaki Ƙaramar Hukumar Gubio, mai tazarar kilomita 70 daga Maiduguri, kuma tun a lokacin ne yake hannunsu.
A lokacin dai, mayakan sun ce sun kai wannan farmakin ne domin su kwashi kayan abinci da man fetur daga wata motar kungiyar ayyukan jinkai a Jihar ta Borno.
Wancan farmakin dai ya tilasta wa mazauna garin arcewa daga garin domin neman tsira da rayukansu, inda sai bayan ficewar ’yan ta’addan jama’a suka koma gidajensu.