✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ISWAP ta kori ’yan Boko Haram daga zama ’ya’yanta kan zargin zagon kasa

ISWAP na zargin tsoffin 'yan Boko Haram din da hada baki da sojoji

Kungiyar yan taadda ta ISWAP ta kori tsoffin yan kungiyar Boko Haram wadanda a baya suka sauya sheka suka kuma yi mubaya’a gareta, bayan rasuwar shugabansu, Abubakar Shekau.

Aminiya ra rawaito cewa Abubakar Shekau, tsohon Shugaban Boko Haram, ya kashe kansa a wata arangama da wasu manyan kwamandojin ISWAP da suka sauya sheka a watan Yunin 2021.

Makonni da rasuwarsa, dubban ’yan Boko Haram sun yi mubaya’a ga kungiyar ISWAP karkashin Aba Ibrahim Al-Hashimiyil AlKhuraishi, wanda suka nada da murya daya a matsayin ‘Khalifan Musulmai’, wanda aka fassara da “Shugaban dukkan Musulmi”.

Aminiya ta samu labarin cewa watanni 19 da hadewar su, shugabannin ISWAP sun shaida wa Boko Haram cewa lokaci ya yi da za su fice, saboda sun yi imanin cewa akwai barayi cikinsu da ke yaki da kungiyoyin a boye.

Hare-haren da rundunar Sojin Najeriya ke kai wa ta hanyar leken asiri, sun yi sanadiyar mutuwar daruruwan ’yan ta’adda tare da shafe matsugunansu a cikin ‘yan watannin da suka gabata.

Wata majiya mai tushe ta shaida cewa kungiyar ISWAP ta ci gaba da hasashen cewa hare-haren wuce gona da iri da sojojin Najeriya ke kai wa, ba irin wadanda aka saba gani ba ne kuma suna zargin juna a tsakanin su da zargin suna kai rahoto ga jami’an na soja a asirce.

Sun bayar da hujjar ne biyo bayan fafatawar da ta barke tsakanin kungiyar Boko Haram ta Bakoura Doro (Abou Oumaymah) – bangaren Boko Haram da ke jagorantar munanan hare-hare a kan ’yan ta’addar ISWAP.

Yayin da yake jawabi ga mayakan da iyalansu a Timbuktu Triangle, Shugaban ISWAP, Abbah Shuwa wanda aka fi sani da Ba’a Shuwa, ya zargi ’yan Boko Haram da suka sauya sheka da fuska biyu.

Ya ce: “Kuna iya cewa kuna tare da sojojin Halifa amma zuciyarku da ruhinku suna tare da Murtad da Khawarij.

“Har yanzu kuna biyayya ga kungiyar Boko Haram ta Abubakar Shekau, har yanzu kuna goyon bayan Abou Oumaymah, da Ali Ngulde, don yakar mu.”

Shuwa ya kuma zargi mayakan na Boko Haram da hada kai da ’yan Boko Haram da suka tuba domin fallasa hare-haren da suka shirya wanda a lokuta da dama ke haifar da gazawa.

Ya bayar da misali da hare-haren 14 da 23 ga watan Janairun 2023, wadanda suka yi sanadin kashe dimbin ’yan kungiyar tare da kwato manyan motoci kirar Hilux da makamai da dama da sojojin Najeriya suka yi a Damboa.

Don haka ya yi gargadin cewa su mika makamansu su fice nan take ko kuma su fuskanci fushin kungiyar.

Sakamakon haka, a ranar 24 ga watan Janairu, ISWAP karkashin jagorancin Ba’a Shuwa, ta kai hare-hare a matsugunan Boko Haram a Mantari, Gabchari da Maimusari a yankin Bama, inda suka kashe mayakan da dama tare da tilasta wa wasu tserewa zuwa yankin Banki.

Aminiya ta gano cewar, tsoron halaka su a fagen fama ya tilasta wa kwamandojin Boko Haram da iyalansu barin aikinsu tare da mika wuya ga sojoji.

Da yawa daga cikin mayakan sun kuma mika makamansu sakamakon tsananin yunwa da kuma kusan rashin samun damar shan magunguna ko cin abinci na yau da kullun.

A bisa dukkan alamu dai karfin fadan nasu ya ragu matuka inda ragowar suka bar sansanoni daban-daban, inda suka bar wasu ’yan ta’adda wadanda ba su da wata dama ta ko dai sojojin Najeriya ko kuma su kansu ’yan ta’addan gudun rasa ransu.