Ministan Tsaron Isra’ila Itamar Ben-Gvi, ya umarci ’yan sandan kasar da su cire tutocin Falasdinu daga dukkan gine-ginen gwamnati, inda ta bayyana tutar a matsayin ta “ta’addanci”.
Isra’ila dai kai tsaye ba ta haramta sanya tutocin Falasdinu ba, amma ’yan sanda da sojoji na da ikon cire su a duk lokacin da suka ga za ta kasance barazana gare su.
- Hatsari ya ci mutum 2, wasu 5 sun jikkata a hanyar Abuja-Kaduna
- An yi ca kan matar da ta ‘sayar’ da kuli-kulin N1bn
Umarnin Ministan na zuwa ne ranar Lahadi, kodayake ba sabon abu ba ne, amma Falasdinawa na kallonsa a matsayin wani yunkuri na murkushe su da karfin tuwo.
Kazalika, ba da umarnin ya biyo wata zazzafar zanga-zangar kin jinin Isra’ila da aka yi a birnin Tel Aviv ranar Asabar, inda wasu daga cikin wadanda suka yi suka rika daga tutocin Falasdinun.
Masu zanga-zangar dai sun rika yi Allah-wadai da gwamnatin Fira Minista Benjamen Netanyahu, inda suka rika neman a rika yin daidaito tsakanin Yahudawa da Falasdinu.
Adadin Falasdinawan da suke zaune a Isra’ila dai sun kai kusan daya bisa biyar na yawan jama’ar kasar, kuma galibinsu tsatson Falasdinawan da suka ki barin kasar bayan an kirkire ta a 1948.