✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isma’ila Surajo: Matashi mai fasahar kere-kere

Aminiya ta yi kicibis da wani matashi mai suna Isma’ila Surajo da ya dauki motar tarakta da ya kera zuwa ofishin Hukumar Ilimin Bai-Daya (UBEB)…

Aminiya ta yi kicibis da wani matashi mai suna Isma’ila Surajo da ya dauki motar tarakta da ya kera zuwa ofishin Hukumar Ilimin Bai-Daya (UBEB) ta Birnin Tarayya Abuja. Ya bayyana yadda ya faro ayyukan kere-kere da kuma burin da yake son ya cimma a rayuwa:

 

Wane ne kai?

Sunana Isma’ila Surajo. Ni dan asalin garin Rubochi ne da ke nan Abuja. Kuma dan kabilar Gbagyi, ina da shekara 22. Na yi makarantar firamare a LEA Ope da ke Rubochi sai karamar sakandaren Rubochi. Bayan nan sai na wuce babbar  sakandaren kimiyya da kere-kere ta gwamnati da ke Area 3 Garki Abuja. Na gama sakandare a shekarar 2016 sai dai ban samu gurbin shiga makarata ta gaba ba saboda matsalar rashin kyan jarrabawar sakandare da na fuskanta

Wane lokaci ne ka fara sha’awar yin kere-kere?

Tun ina aji biyu a makarantar firamare. Malamanmu na sa mu yin jarrabawar gida (homework) a kan kera wani abu da kwali, sai mu kawo makaranta. Nakan ci gaba da yin na kashin kaina har lokacin hutu sai abokaina su saya. To da na shiga karamar sakandare sai na shiga wata gasa ta kananan makarantun sakadare na Abuja a bangaren kulob na masu karanta darasin kimiyya da kere-kere, inda na zo na daya. To daga wancan lokaci ne sai aka ce ba a bukatar na kwali, a nan ne na fara amfani da gorar-ruwa wajen kera abu. Na shiga wata gasa ta Hukumar UBEB, a nan ma na zo na daya a yankin Abuja. Bayan nan sai wata gasar da Hukumar Talabijn ta Kasa (NTA )ta shirya a nan Abuja a shekarar  2013 inda na zo na daya.

Ko za ka lisaffa abubuwan da ka kera zuwa yanzu?

Na farko dai akwai jirgin kasa da mutum-mutumin baban bola tare da baro da bai bukatar matuki da injin buga bulo 3 a lokaci guda da karamar motar tarakta da za ka iya yin noma da ita da shuka da kuma daukar amfanin gona zuwa wani waje, sai kuma motocin aikin hanya kamar ta rusau da ta daukar kasa ko yin lebur da kuma tifar daukar kasar. Ga kuma budaddiyar motar tirela don daukar taraktocin. Akwai kuma babban babur na ma’aikatan tsaro.

Kamar wadanne abubuwa ne ka yi amfani da su a kera na’urorin?

Akwai abin da a ke kira electric motor a Turance na’ura ce mai yanayin injin fanka da ke amfani da batur don juya taya ko tankwara na’ura ta aikata abin da ake son a yi. Nakan saye su ne daga wajen ’yan bola. Akwai kuma taya da nake yi daga takalman silifas masu kauri.

Wane alheri ka samu a wannan abu da kasa a gaba

A gaskiya na samu alheri mai yawa. Na farko dai na samu kyautar na’urar kwamfuta. Na wakilci kasar nan a gasar ’yan makaratar sakandare bangaren kimiyya da kere-kere a kasar Brazil wanda UBEB ta dauki nauyi zuwanmu. Nakan kuma samu gudunmawar jama’a jifa-jifa wadda da ita nake sayen kayan da nake amfani da su.

Wane kalubale kake fuskanta?

Akwai rashin isasshen kudi da wajen aiki da kuma kayan aikin. Ina bukatar wadanda za su rika daukar nauyin aikin da nake yi.

Zuwa yanzu ko akwai wani tallafi da ka samu daga hukuma ko kungiya?

Akwai wata kungiya mai suna Help Life Foundation ta taimaka mini, da Abuja Chamber of Commerce and Industries sai kuma Hukumar UBEB. Daga cikin gudunmawar da ni kuma na yi ga makarantata, baya ga ciyo mata kofuna a gasa a wannan bangare, na kera wata na’urar sadarwa ta amsa kuwwa na mika ta ga makaratar a matsayin project dina a lokacin kammala makarantar da a ke amfani da ita a yayin taro.

Wane buri kake da shi?

Ina fata in samu wadanda za su dauki nauyin ci gaban karatuna don bunkasa ilimi a wannan bangare saboda burina shi ne in ga na samu shiga jami’ar kere-kere ta yadda zan zama injiniyan kanikanci.