Kungiyar ISIS ta wallafa wani bidiyo da ta ce ta kashe wasu Kiristoci 20 a Jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Daya daga cikin ’yan kungiyar da ya rufe fuskarsa, cikin harshen Hausa, ya ce kisan fansa ce suka dauka kan kashe jagoransu na Gabas ta Tsakiya da aka yi a 2021.
- Rarrabuwar kai kan karba-karba ya jawo dage taron PDP
- Wata zai yi rashin lafiya a Najeriya ranar Litinin — Masana
Kafar Yada Labarai ta BBC dai ta gaza tantance hakikanin wajen da aka dauki bidiyan ko sahihancin abin da ya kunsa.
An dai wallafa shi ne a shafin wallafa labaran kungiyar, inda aka nuno wasu mutum uku suna sanye da kayan gida.
Kungiyar ta’addancin wacce ke ayyukanta a kusa da Tafkin Chadi da sunan ISWAP, da kuma kungiyar Boko Haram dai na asarar mambobi saboda luguden wuta daga sojojin kasashen duniya daban-daban.
Ya zuwa yanzu dai hukumomi ba su ce komai kan bidiyan ba, sai dai ko a baya dai luguden wuta daga sojin kan haddasa bidiyan farfaganda na barazana daga kungiyoyin ‘yan ta’addan.