✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISIS ta fara yunkurin hana Gasar Cin Kofin Duniya a Rasha

kungiyar ISIS ta ce tana yunkurin ganin ta hana gudanar da Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a badi a Rasha ko ta…

kungiyar ISIS ta ce tana yunkurin ganin ta hana gudanar da Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a badi a Rasha ko ta halin kaka.

Gasar wacce za ta gudana a tsakanin ranakun 14 ga Yuni zuwa 15 ga Yulin 2018, kungiyar ta ce za ta kai hare-hare ne a daukacin filayen wasnani 11 da za a yi amfani da su a lokacin gasar ta badi.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafin sadarwarta na yanar gizo, an ga wani hoton bidiyon daya daga cikin dakarun kungiyar ISIS rike da bindigogi da kuma bama-bamai a tsaye a gaban wani filin wasa (stadium) da ba a tantance ba yana bayanin yadda kungiyarsa ke yunkurin kai hare-hare a filayen wasanni na Rasha a badi.

kungiyar dai ta yi gargadi ga ’yan wasa da jami’ansu da kuma daukacin ’yan kallo da su kaurace wa gasar don ganin sun tsira da ransu. 

ISIS dai ba ta ga-maciji da Shugaban Rasha bladimir Putin musamman ganin yadda ya daure wa gwamnatin Siriya gindi wajen yakar kungiyarsu da hakan ta sa suke kokarin daukar fansa a lokacin gasar cin kofin duniya da za ta gudana a Rasha a badi.

Idan za a tuna, a watan Afrilun bana ne kungiyar ta kai wani kari a Rasha ta hanyar  ajiye wata jaka a kan hanya mai shake da bam da hakan ya sa akalla mutum 14 suka halaka a wancan lokaci.