Masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a farfajiyar Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya na sane da takaddamar Iro-Dogon Turke da Ladanin-Mur na kasar Rasha, musamman kan yadda masu harbi da bindiga daga Turakun tarairayar uwa-da ’ya’ya suka kakkabo tsuntsun saman artabun Rashawa. Wannan takaddama da cece-ku-ce kamar yadda kafafen yada batutuwa suka nusar da duniya ta dauki sabuwar alkibla, inda mahukuntan birnin Masu-koko suka kakaba wa Turakun-tarairayar-uwa-da-’ya’ya takunkumi. Kuma a batutuwan baya-bayan nan da aka bijiro da su, an tabbatar da cewa, kasar Ladanin-Mur ta harbi kwale-kwalen Turakun-tarairayar-uwa-da-’ya’ya na kamun tarwada.
Iro-Dogon Turke dai bai ce uffan ba, domin jiga-jigan gwamnatinsa da sauran mahukuntan birnin An-kakara-kara ke mayar da martani a duk lokacin da wata takaddama ta taso. Kuma an tabbatar da cewa, kasar Uban-Mama jikan Kenyawa jagoran Amurkawa ita ta bai wa mahukuntan Turakun-tarairayar-uwa-da-’ya’ya bayanin sirrrin sagaraftun tsuntsun saman Rashawa ta sararin samaniyarta, a yunkurinta na kai hari a kasar Siriyawa.
Siriyawa dai sun saduda a hannun Bashiru dan Asadu, inda har yanzu sai jefa azargagiyar zarge-zarge ake yi, tsakanin masu tayar da kayar baya da suka samu mafaka a Turakun-tarairayar-uwa-da-’ya’ya da magoya bayan Bashiru dan Asadu, wadanda a halin yanzu artabun yake-yake ya haifar musu da yin kaura daga kasarsu ta haihuwa; wasu sun turke a Turakun-tarairayar uwa da ’ya’ya, wasu kuwa sun nausa zuwa Turai, inda ake ta kokarin ture su, ko ma in ce sun warwatsu cikin nahiyoyin duniya.
Babban abin da wannan makaranta ke kokarin nusar da Iro-Dogon Turke, ita ce wakarmu ta tatsuniya, idan manyan dawa na fafatawa:
Zaki bari, damisa bari,
Fadan ku na manya
Wa yake shiga?
Sai wawa, sai mahaukaci!
Kai har aka gama rera wannan waka a zamanin muna ’yan dugwi-dugwi ban fasko inda aka dosa ba, domin na dauka kawai nisahadantar da mu ake yi, don mu rage kiriniya irin ta man-kaza. Sai ga shi yanzu da lokaci ya yi na fasko cewa, wannan waka tamkar faskaren ma’ana ce ga karairairaye-karairayen maganganun masu murguda baki kamar sun ci kilishi, sun kuma kanga gilashi suna ta yaren Ingilishi, inda sukan furta cewa: Idan giwaye karamin lauje na artabu ciyawa ce kawai ke jigata. Ina ganin ba za a rasa ’yan makarantarmu da ke da masaniyar cewa, “tatsuniya makaranta ce ta dan Bahaushe da ya koya wa dan sa karatun zaman duniya, tun kafin addini ya shige shi.” Ni dai haka na ji a wajen masana.
Batu na ingarman karfen karafa idan mutane suka yi la’akari da batutuwan da ke fitowa daga kasar Iro-Dogon- Turke, al’amura na nuni da cewa, ‘tamkar shi ya balgato fuka-fukan tsuntsun saman Rashawa don kawai ya ga yaya mahukuntan birnin Masu-koko za su yi.
Koma dai mece ce manufar Iro-Dogon Turke, wannan takun saka da ya shiga da Ladanin-Mur, idan ya bari Rashawa suka ci gaba da sha masa mur, tabbas talakawansa za su dandana kudarsu.
Irin wannan dambarwar wasan Samson-siya-siya da mahukunta ke yi da kwakwalen talakawa shi ke kara ruruta wutar rikice-rikice, har ta kai ga an cako tsiyatakun tsikarin al’umma a kuma yi ta dawurwurin yadda za a warware kullin bakin zaren.
Haurobiyawa, musamman ’yan makaranta lallai ya kamata mu dauki darasi, ta yadda za mu zarta ’yan kwana-kwana iya kashe wuta da balbalin bala’in rikici. Babban abin da nake son nusar da mu, shi ne, mu daina bari wani ya bautar da tunaninmu, kada mu rika yi wa shugabanni, musamman wadanda ke ikirarin yada ilimin addini biyayya a makance, don kada mu afka rami. Kada mu bari kasarmu ta zama jujin jibge akidu domin daukacin abin da mabiya addinai ke ja-in-ja a kai al’amura ne da ba su kai girman Sunnah ba balle farilla. Kuma duk da cewa, ni ba na cikin manyan malaman Haurobiya masu tumin rawuna, ina ganin lokaci ya yi da kowace manhajar koyar da ilimi za ta hau kan doron kawar da juhala, don tabbatar da adala a tsakanin al’umma. Sannan mu rika bibiyar kundin al’amuran da suka wanzu a tsawon zamunna, ta yadda za mu zauna babu zaminiya, tamkar a yankin Mwanza na kasar Tanzaniya; mu kuma zama masu tarairayar uwa da ’ya’yanta a turakunmu, amma ba irin na Iro-Dogon turke ba; domin shi burinsa kasarsa ta shiga gungun kasashen Turawa, amma sai kokarin ture shi ake ta yi, shi kuwa ya ki yin zuciya ya yi na-damo..
’Yan makaranta a irin fahimtata, ina ganin daukacin addinin Kadaita Mahalicci da ibada ai “amru ne da nahayu,’ wato dai hani da umarni, musamman dangane da kyakkyawa ko mummuna da al’umma ke tsuwurwurtawa da hannayensu. Kuma tun muna ’yan dugwi-dugwi muke jin ana ta karanta wa masu koyon karatun addini a Lahallari, cewa, “Wa ya kifa inda amrihi, wa nahayihi,” wato ka tsayu inda aka umarce ka, ka kuma hanu da abin da aka hane ka.’ Wannan dai ita ce ka’ida. Kuma an nusar da mu a cikin kawa’idi, cewa, daukacin malaman mazahabobi sun zo ne domin yaye rikice-rikice, wato Liyakashifa mabika minal ashkali.
Sannan malaman soro da masu tsayuwa a kan mumbari da masu gargadi da bushari sun sha nusar da mu cewa, “Hikima dukiyar mumini ce ta bace, don haka sai ya tsince ta duk inda ya gan ta,” (matukar ba ta saba wa dokokin Mai-duka ba).
Uwa-uba dai mu bibiyi al’amuran da ke wakana a wasu kasashen da ke cikin nahiyoyin wannan duniyar, ta yadda za mu shafa wa gemun Haurobiya ruwa, tunda na ’yan uwanmu da ke wasu kasashe ya kama da wuta; wasu bisa ganganci, wasu kuwa an kulla musu makirci.
Abin da ya rage mana tun kafin a jefa mu cikin tsomomuwa, wajibi ne mu tarairayi juna, kada mu jawo rikicin da zai mamaye ’yan uwanmu, wanda duk ya hango dan uwansa na tafka ta’asa a kwanon tasarsa, to ya iya difara masa gurasa gami da masa, ga wasa-wasa a zuba a kwanon tasa ’yan kasa su yi ta kwasa, ba wani wasa. Da fatan an baje na mujiya, an buda na-zomo don jin abin da zai tsirar da gangar jiki. Domin fitina ta yi likimo, idan kuwa ta farka sai ta mamaye kowa. Muna rokon Mai-duka da Ya rangwanta mana a cikin al’amuranmu, ta yadda za mu daina sha wa juna mur, tamkar yadda aka karke tsakanin Iro-Dogon Turke da Ladanin-Mur na birnin Masu-koko.
Iro-Dogon Turke
Masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a farfajiyar Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya na sane da takaddamar Iro-Dogon Turke da Ladanin-Mur…