✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

IPOB: Mahara sun kashe sojoji 5 da farar hula 1 a Anambra

Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’ya’yan haramtacciyar kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra (IPOB) ne, sun hallaka sojoji biyar da farin hula daya a…

Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’ya’yan haramtacciyar kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra (IPOB) ne, sun hallaka sojoji biyar da farin hula daya a Karamar Hukumar Orumba ta Kudu da ke jihar Anambra.

Wani ganau ya ce da karfe 1:00 na rana zuwa 2:00 sojojin suka iso wurin a mota kirar Toyota Sienna domin sintiri, sai kawai maharan suka far musu.

Sai dai kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, Ikenga Tochukwu, ya ce, “Ba zan iya tabbatarwa ko an kashe sojoji ba, amma na sa an samu harbe-habe a titin Umunze da ke daura da wani banki,” in ji shi.

Ikenga ya ce tuni rundunar ta tura jami’anta yankin, domin daidaita al’amura.

A baya-bayan nan dai ana ta samun kashe-kashe a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, wanda ake alakantawa da IPOB din, duk da ta sha musanta zargin.