✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Inganta fiton kaya zai kara wa Najeriya samun kudin shiga’

Aminiya: Me ye za ayi don inganta harkar samun kudin fito a kasar nan a matsayin ka na mai shigo da kayayyaki?Yakamata gwamnatin tarayya ta…

Aminiya: Me ye za ayi don inganta harkar samun kudin fito a kasar nan a matsayin ka na mai shigo da kayayyaki?
Yakamata gwamnatin tarayya ta inganta harkar samun kudinta a gabar tekuna da sauransu domin ta samu karin kudaden shiga gadan-gadan. Wannan zai yiwu ne ta hanyar gyara yadda ake tantancewa da kuma kula da cewa ba a raina kadan ba. Dalilan sun hada da sanin cewa idan an lalata kafafen samun kudin shiga a Najeriya, jama’a za su koma yin fito ta wasu kasashe na daban.
Domin idan ana biyan naira dubu 200 a Najeriya ga mota, to idan an biyo ta Kwatano, sai ka biya naira dubu 50. Idan ka lissafa yawan motocin da za a biya za ka ga Najeriya na matukar yin asara. Bugu da kari mutanen Kwatano suna samun aikin yi ta hanyar ba da hayan dakunan otel, masu abinci da masu ruwan sha da kudin shiga kasar da dai sauransu.
 Aminiya: Ko za ka yi karin bayani?
Ida Najeriya na karban naira dubu 50 ga kowace motar da aka taba hawa a waje sannan naira dubu 100 ga sabon mota, idan an yi jimilla, ba karamin kudi ba ne. Domin rashin yin hakan ya sa ba gyaira-ba-sabar  ’yan Najeriya suke shigo da kaya ta wasu kasashe wanda hakan ya sa Najeriya na asarar kudin da ya kai biliyoyin nairori.
Aminiya: Ta yaya ake kara jawo wa kasa asarar kudin shiga da kuma yadda za a magance haka?
Hanyar da ake ci wa Najeriya dudduge sun hada da yadda ake kara bude sabbin barayin hanyoyin da ’yan sumugal ke ketawa a dazuzzuka da yawa. Maganin haka shine a rage kudin da ake tatsa daga hannun ’yan kasuwa don su biyo hanyoyin da ’yan kasa za su samu aikin yi ta hanyar ta yin kasuwanci a gefen tituna don kyauyuka su bunkasa.
Aminiya: Shin ko ana yi maka satan kaya?
A’a domin ina yin hayan Kwantaina (Sunduki) don asa mini kaya ban budewahar sai sun iso inda nake hada-hada. Amma wadanda ba su sanya kayansu a Kwantaina ba, to shi ne ake cewa “roro” wato wanda barayin waff wadanda aka fi sani da suna “Wharf Rat” suke sace wa.
 Aminiya: Shingaye nawa kuke samu daga Legas zuwa Abuja?
Ai abin babu dadin ji ko kadan, domin idan mun fito sai mun sallami soja da ’yan sanda da kuma kwastam. Don haka idan mun zo sayarwa sai mu sa abin da muka yi asara a cikin lissafi a cikin kayan da muke tallatawa.