Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta ce za ta mayar da wuraren kada kuri’a kimanin 3,148 dake jihar Kano zuwa cikakkun rumfunan zabe.
Kwamishinan hukumar a Kano, Farfesa Riskwa A. Shehu ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan harkar zabe da hukumar ta shirya ranar Asabar a Kano.
Ya ce hukumar ta yanke shawarar daukar matakin ne da nufin rage cunkoso tare da samar da tsari a rumfunan zaben.
Farfesa Shehu ya ce, “Akwai masu zabe wadanda suke da rijista sama da miliyan biyar a jihar Kano da kuma rumfunan zabe 8,074, sai kananan wuraren kada kuri’a 3,148.
“Daga cikin irin sauye-sauyen da muke yi, INEC ta bullo da tsarin fadada rumfunan zabe, kuma tuni har kwamitin da aka kafa ya ba da shawarar mayar da irin wadannan wurare cikakkun rumfunan zabe.
“Da zarar an amince da hakan, jihar Kano za ta zama tana da rumfunan zabe 11,222 kenan,” inji shi.
Sai dai ya ce za a kafa irin wadannan rumfunan ne a gine-ginen gwamnati kawai, inda ya ce ba za a yi amfani da gidajen mutane ko na ’yan siyasa, fadojin sarakunan gargajiya ko wuraren ibada ba.
Shima da yake jawabi, Kwamishinan hukumar na kasa mai kula da wayar da kan jama’a, Barista Festus Okoye ya ce bukatar karin rumfunan ta biyo bayan karuwar yawan jama’a da kuma kafuwar sabbin unguwanni da garuruwa ne a sassa da dama na Najeriya.
Ya ce rabon da INEC ta kirkiri sabbin rumfunan zabe tun shekarar 1996, lokacin Najeriya na da masu zabe miliyan 50, amma yanzu ya ce adadin ya haura miliyan 84.
Barista Festus ya kuma ce nan da ranar 28 ga watan Yuni hukumar za ta dawo da rijistar masu zabe.
Taron dai ya sami halartar wakilan jam’iyyun siyasa daban-daban daga jihar, shugabannin dukkan hukumomin tsaro, shugabannin addinai da sarakunan gargajiya da kuma kungiyoyi masu zaman kansu da na fararen hula.