✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ina son harkar da’awa kan abin da ya shafi mata —Zainab Ja’afar

Ina da burin Allah ya sa na yi kyakkyawar rayuwa a nan duniya na kuma rabauta a gobe kiyama.

’Yar marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, Malama Zainab, burinta shi ne ta ga ta yi karatu mai zurfi a a fannin da’awah musamman a kan abin da ya shafi mata.

Malamar ta yi wannan jawabi ne lokacin da take tattauna wa da kafar yada labarai ta BBC Hausa a wata hira ta musamman da aka yi da ita.

Ta bayyana cewa tana son ta wayi gari ta ga Allah ya azurta ta da ilimi mai zurfi da zai yi wa ’yan uwanta mata tasiri wurin kawo gyara da sauye-sauye a kan munanan dabi’u ko halayya ko rashin tarbiyya a tsakaninsu a kowane mataki na rayuwa.

Ta kara da cewa, “ina kuma burin Allah ya sa na yi kyakkyawar rayuwa a nan duniya na kuma samu dacewa a gobe kiyama.”

Ana iya tuna cewa a baya bayan nan an bai wa Malama Zainab matsayin Shugabar Kungiyar Mata ta Nisa’us Sunna reshen Jihar Kano.

%d bloggers like this: