✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina makomar su Sanata Shekarau bayan hukuncin Kotun Koli?

Ta tabbata Abdullahi Abbas shi ne shugaban APC a Kano, bayan hukuncin kotun koli.

Wace dabara ta rage wa tsagin Sanata Shekarau bayan tsagin Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kayar da su a Kotun Koli?

Wannan na daga cikin irin tunanin da zai zo wa mutane da dama, shin su Sanata Shekarau za su mika wuya ga shugabancin Abdullahi Abbas ko kuma da sauran rina a kaba?

Hukuncin Kotun Koli

A ranar Juma’a ne Kotun Koli ta tabbatar da tsagin Ganduje a matsayin halastaccin shugabancin Jam’iyyar APC Reshen Jihar Kano.

Wannan na zuwa ne bayan daukaka kara da tsagin tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Ibrahim Shekarau ya yi na neman ta ayyana Haruna Ibrahim Danzago a matsayin shugaban jam’iyyar APC na jihar.

Kwamitin Alkalan kotun mai mambobi biyar, karkashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a.

A cewar Mai Shari’a Okoro, Kotun Daukaka Karar da ta saurari karar da aka gabarta mata da farko ba ta da hurumin yin haka, don haka karar ta zama abar korewa.

Har wa yau, Kotun Kolin ta ce hukuncin da ta yanke ya shafi sauran kararraki biyun da aka daukaka a shari’ar.

Idan ba a manta ba, a watan Fabrairu kotun daukaka kara ta kori kararraki ukun da aka gabatar mata, saboda rashin cika sharudda wajen daukaka su, tare da cewa matsalar ta cikin gida ce wadda ba sai an fita waje don magancewa ba.

Yadda rikicin ya samo asali

Rikicin shugabancin Jam’iyyar APC a Jihar Kano ya samo asali ne tun lokacin da tsagin Sanara Shekarau ya bijire wa tsagin Gwamna Ganduje, wanda Abdullahi Abbas ke a matsayin shugaban jami’iyyar a jihar.

Lamarin dai ya kai ga kowanne daga cikin bangarorin biyu ya gudanar da zabensa na shugabannin jam’iyya, wanda tsagin Ganduje ya zabi Abdullahi Abbas, bangaren Shekarau kuma ya zabi Haruna Dan Zago a matsayinsa shugaban jam’iyya.

Tsagin Sanata Shekarau da ya kunshi shi kansa Sanata Shekarau da Sanata Barau I. Jibrin da dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazabar Birni, Sha’aban Ibrahim Sharada, sun sanya kafar wando daya da bangaren gwamnatin jihar.

A baya dangantakarsu ta yi tsami matuka, har ta kai ga an mayar da bangaren Shekarau saniyar ware, aka gayyatar tsagin Shekarau duk wani taron APC a jihar.

Jita-jitar sulhu

A baya-bayan nan an rika yada cewa Shekarau ya ziyarci Gwamna Ganduje don sasantawa kan abubuwan da suka faru, bayan hukuncin da Kotun Kolin ta yanke a ranar Juma’a.

Labarin da babu tabbaci a kansa, ya bayyana cewa Sanata Shekarau ya bukaci Ganduje ya ba shi damar sake komawa kujerarsa ta Sanatan Kano ta Tsakiya.

Amma ko ma mene ne, Hausawa na cewa ‘lokaci alkali’, kazalika, ‘idan ta yi tsami a ji me ake ciki’.

APC a Kano na tattare da kalubale

APC a Jihar Kano kamar sauran jam’iyyu na da kalubale da ke tunkaro ta musamman idan aka kammala zaben fidda-gwani.

A jihar, akalla ’yan takara 10 ne ke zawarcin kujerar gwamnan jihar don maye gurbin  Ganduje a 2023.

Kadan daga cikinsu sun hada da mataimakin gwamnan Jihar Nasiru Yusuf Gawuna da Kwamishinan Kananan Hukumomi, Murtala Sulen Garo da A.A. Zaura da Salihu Sagir Takai da sauransu.

Tuni wasu ke ganin za a kwashi ’yan kallo a wajen fitar da wanda zai maye gurbin gwamnan jihar mai ci a yanzu.

Wasu kuma na ganin akwai yiwuwar a daidaita tsakanin wasu ’yan takarar don kai jam’iyyar ta APC gaci a 2023, duba da yadda sabuwar jam’iyyar su Kwankwaso ta NNPP ke kara karfi a jihar.