✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ina dan wasan da ya zura kwallon da Najeriya ta lashe AFCON 2013, Sunday Mba, yake?

Da alama har yanzu bai samu kulob ba, kuma shekarunsa sun ja.

Sunday Mba dan wasan tawagar Najeriya ne da ya zura kwallo a ragar Burkina Faso a wasan karshe na Gasar Cin Kofin Afirka ta shekarar 2013.

Da wannan kwallon da ya zura ne Najeriya ta lashe gasar a lokacin yana kwallo a kungiyar Enugu Rangers ta Firimiyar Najeriya a matsayin dan wasan aro daga kungiyar Warri Wolves.

Nasarar da Mba ya samu aka yi tunanin zai bude wa masu taka leda a Firimiyar Najeriya kofar samun damar shiga Super Eagles din.

Haka kuma, an yi tunanin daga lokacin tauraronsa zai haskaka a duniya, sai dai binciken Aminiya ya gano cewa a yanzu haka dan wasan yana zaune ne ba tare da kulob ba. Kuma Najeriya ba ta gayyatar sa.

Bayan AFCON 2013, dan wasan ya koma kungiyar Bastia CA ta Faransa ne, daga shekarar 2014 zuwa 2015.

A shekarar 2015 ya koma kungiyar Yeni Malatyaspor ta Turkiyya, inda ya taka leda zuwa 2017, daga nan kuma kungiyar ta sallame shi.

Tun daga wannan lokaci bai kara samun kulob ba, har zuwa shekarar 2019 inda ya fito ya bayyana wa duniya cewa yana neman kulob din da zai cigaba da taka leda.

A bangaren buga wa Najeriya wasa kuwa, tun bayan Gasar Cin Kofin Afirka din ta 2013 da ta fito da shi duniya, sai kuma Gasar FIFA Confederations da ake bugawa tsakanin kasashen da suka lashe kofunan nahiyarsu, ba a sake jin duriyarsa ba a tawagar Super Eagles.

Uwa uba, da alama har yanzu bai samu kulob ba, kuma yanzu shekarunsa sun ja matuka.