Fadar Shugaban Kasa ta bayyana yakininta cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai mika mulki ne ga sabuwar gwamnatin jam’iyyarsa ta APC bayan zabe mai zuwa na 2023.
Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa, Garba Shehu, shi ne ya bayyana haka ne ga manema labarai jim kadan bayan fitowa daga taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya, a ranar Laraba.
- Gwamnatin Kwara ta gargadi makarantu kan hana sanya Hijabi
- NAJERIYA A YAU: Zaben 2023: Wa zai kai Najeriya tudun mun-tsira
- Paul-Henri Damiba: Wane ne sabon Shugaban Burkina Faso?
Garba Shehu ya bayyana yakininsa game da nasarar jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2023 ne a yayin da yake amsa tambayoyi a kan dakatar da cire tallafin man fetur da Shugaba Buhari ya yi, yana mai cewa shugaban kasar ya yi abin da ya dace.
“Ina da tabbacin cewa gwamnatin APC ce za ta sake hawa mulki a 2023, kuma Shugaba Buhari zai mika mata mulki idan wa’adinsa ya cika,” a cewar Garba Shehu.
Dambarwar makomar tallafin man fetur
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, shi ne ya fara bayyana cewa shugaba Buhari bai taba bayar da umarnin janye tallafin man fetur ga kowa ba.
Bayanan na Sanata Ahmad Lawan sun zo ne bayan da farko Gwamnatin Tarayya ta ce a watan Fabrairu ya kamata a dakatar da biyan tallafin mai, kamar yadda sabuwar Dokar Man Fetur (PIA) ta tanadar.
Ta kuma bayyana shirinta na biyan ’yan Najeriya abin da ta kira ‘kudin mota’ na tsawon wata shida bayan janye tallafin, amma ta ce zuwa watan Yuni za ta yanke shawara a kan makomar tallafin man.
An yi ta zargin gwamnatin da shirin janye tallafin man a watan Fabrairu mai kamawa, wanda hakan ya fusata ’yan Najeriya da suke ganin janye tallafin zai kawo karin tsadar man fetur din da kuma jefa rayuwarsu a cikin matsi fiye da wanda suke ciki a halin yanzu.
A kan haka ne Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), ta yi barazanar tsunduma zanga-zanga a fadin kasar don nuna adawa ga shirin Gwamnatin Tarayya na janye tallafin.
Sai dai a ranar Litinin Gwamnatin Tarayya ta lashe amanta, inda ta bayyana cewa ta dakatar da janye tallafin man fetur din, sai bayan wata 16 masu zuwa.
Amma wasu masu sharhi kan harkokin siyasa, na ganin dakatar da batun na da alaka da babban zaben 2023 da ke karatowa.
Sun bayyana cewa gwamnatin ta yi dage lokacin soke tallafin ne domin kada a yi amfani da janye tallafin man wajen yakar ta a zaben 2023.
Sai dai kuma gwamnatin da za ta gaji Buhari za ta yi karo da matsalar, lura da cewa wa’adin zai kare ne bayan wata biyu da hawan sabuwar gwamnati.