✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina bin NFF albashin watanni biyar – Samson Siasia

Kocin kungiyar kwallon kafa ta U-23 Samson Siasia ya bayyana takaicin ganin yadda ya shafe kimanin watanni biyar ba tare NFF ta biya shi albashi…

Kocin kungiyar kwallon kafa ta U-23 Samson Siasia ya bayyana takaicin ganin yadda ya shafe kimanin watanni biyar ba tare NFF ta biya shi albashi ba.  Kocin ya ce ganin yadda kwantaraginsa ta kare da kungiyar U-23 tun bayan da aka kammala gasar Olamfik inda ya samu nasarar lashe Lambar Tagulla (Bronze) amma har yanzu NFF ta gaza biyansa basussukan albashin watanni biyar da yake bi.
Siasia ya bayyana haka ne a karshen makon jiya a lokacin da ya zanta da manema labarai.
Kocin ya bayyana bacin ransa a kan irin rikon sakainar kashin da Hukumar NFF da Ma’aikatar kula da wasanni ta yi musu a lokacin da suke Atlanta na Amurka don tunkarar gasar Olamfik.
 Ya ce kawo yanzu, ba ya jin zai sake kulla wata yarjejeniya da Hukumar NFF, don bai gamsu da yadda al’amurra ke tafiya a hukumar ba.
Ya ce Allah ne kadai Ya san irin taskun da suka gani shi da ’yan kwallonsa a lokacin da suke Brazil, inda sai da suka zama kamar mabarata amma abin mamaki babu wani hobbasa da Hukumar NFF ta yi game da share musu hawaye.
Kocin ya ce ya zuwa yanzu yana bin NFF bashin albashin watanni biyar, kuma yana fata za ta yi gaggawar biyansa hakkokinsa nan da lokaci kankane.
Tun bayan da aka kammala gasar Olamfik Samson Siasia ya shiga caccakar Ma’aikatar wasanni da Hukumar NFF akan abin kunyar da suka yi da ya janyo ’yan kwallonsa suka shiga halin ni ’ya su a Amurka a gasar Olamfik.  Daga baya ne jami’an Hukumar NFF suka mayar masa da martani ganin yadda yake ci musu fuska a kafofin yada labarai.