✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina basirar ‘yan Najeriya ta bace?

Edita ka ba ni dama in tofa albarkacin bakina game da barkonon tsohuwa da ’yan sanda suka watsa wa ’yan majalisar wakilai. Idan tsabar son…

Edita ka ba ni dama in tofa albarkacin bakina game da barkonon tsohuwa da ’yan sanda suka watsa wa ’yan majalisar wakilai. Idan tsabar son kai da kuma rashin kishin al’umma da ’yan majalisar Najeriya ke yi bai fito fili ba a cikin wannan yudurin, to lallai ba na da sauran kokwanto a kan dadilewar basirar talakan Najeriya. daukacin mutanen da suka rasa rayukansu a Najeriya (musulmi da kirista), da kuma wadanda suka rasa gidajensu da ‘yan uwansu (sama da mutum miliyan daya), ashe ba su kai darajar shugaban majalisa da tawagarsa ba? Tun lokacin da aka sace ’yan matan Chibok ake kuma kashe al’umma ba dare ba rana, babu wani mataki da ’yan majalisa suka yi yundurin dauka sai yanzu da aka watsa musu barkonon tsohuwa? ’Yan majalisa kun ji kunya, wallahi kun ji kunya, kun tabbata marasa kishin al’umma, kun mayar da mu dabbobin daji…. Allah Ya bi ku da anniyarku. Jonathan ko awa 24 bai kamata ya yi a saman mulki ba tun ranar da aka fara kashe mutane ta hanyar dunar badin wake, amma da yake ba ku aka taba ba, sai kuka sanya masa ido.
Ina rodon Allah Ya yi mana maganin  duk cutar da ake yi wa ’yan Najeriya. Ya Allah Ka kawo mana masu tausayinmu. Daga Nasir Abbas Babi 08033186727

Aminiya ta ciri tuta
Aminiya muna godiya kan yadda kuke sanya mana hira da ’yan mazan jiya, wadanda marigayi Dokta Alhaji Mamman Shata ya yi ma wada. Babu wata kafar yada labarai da ta taba tunanin haka. Mu dai a nan kun ciri tuta, wallahi mun gode. AllahYa dara basira. DagaNaseer Nasco Kudan 07035311647.

An raina ’yan majalisa
Harba barkonon tsohuwa a majalisar wakilai, wani babban raini ne da rashin girmamawa ga yan’ majalisar wakilan. Hakan na nuna rashin tasirin yan’ majalissar a dimokuradiyyar Najeriya . Muddin yan’ majalisar ba su tashi tsaye ba, wajen farfado da martabar su da darfin iko, wanda kundin tsarin mulkin dasa ya ba su . Ta hanyar kauce wa dwadayi da hangen makomar siyasar su a gaba. Watakila nan gaba a yi musu cin mutuncin da ya fi haka. Daga Mansoor Said PRP Kano. 07039215954.

Ga Janar Muhammadu Buhari
Salam Editakaba ni dama in mida sadon gaisuwa ga jigo kuma uban ’yan Arewa, Janar Muhammadu Buhari. Allah Ya cika ma burinka. Daga Zahraddeen Al’maus Shifa’a, Jihar Kano 08145515835.

Zuwa ga Edita ina son ku nema min matar aure mai kyan hali, mai tsafta. Daga naku Maharazu Ma.azu 08069630985.

Ga Sufeto Janar Abba
Edita a sanar da Sufeto Janar Abba,  ya bi a hankali ka da ya bari ’yan siyasa su yi amfani da shi.Tsira da mutunci ya fi tsira da tsiya.Don’yan siyasa ba’yan goyo bane ba. Daga IsaDilwala Abuja 07036379291

Ga ’yan Arewa
Kai jama’a wannan shi ne Iya shege,  noma da babbar riga, ba komai yasa na fara wannan karin magana ba sai ganin yadda wasu ‘yan bindiga suka sake kai wa wani mummunan hari a garin Damasak da ke jihar Bornon Najeriya da safiyar ranar Litinin, hasali ma marahan sun shiga garin a motoci kirar Hilud da babura, haka kuma wasu a cikinsu na sanye da kakin soji wasu kuma sanye da kayan gida, lamarin da ya sanya wasu iyalai tuni suka fara tsallaka kogi domin neman mafaka, a Jamhuriyar Nijar da ke makwabtaka da su.  kuma wannan harin na zuwa ne bayan da a cikin makon da ya wuce ‘yan bindigar suka hallaka mutane kusan 100, haba gwamnatin Najeriya da ‘yan majalisunmu, wai yanzu haka za ku ci gaba da zuba ido kuna gani ana tayi mana kisan kiyashi har sai an karar damu baki daya, to masu tada zaune tsaye a jihohinmu na Arewa maso Gabashin Najeriya, wallahi komai nisan jifa dasa zai fado,  kuma komai nisan dare gari zai waye, domin munafuni dodo ne yakan ci mai shi. Daga Adam A. Adam, Garkuwan Matasan Jihar yobe.

Jinjina ga wakilan kwarai
Ina mida jinjinata ga Shugaban Majalisa, Aminu Waziri Tambuwal da Kawu Sumaila da sauran abokan aikinsu bisa tsayawarsu akan sai anyiwa talaka adalci Allah yayi musu jagora amin daga Abubakar umar kofa 08065746051

Gawuna muke so
Assalam dafatan kuna lafiya. Allah ya taimake ku a duk abin da kuka sa a gaba na alheri. Allah ya kareku daga sharrin mahassada. Kamar yadda gwamnatin Jihar Kano ta umarcemu da fita mu yi (RIJISTA), za mu fita mu yi. Amma domin Alh. Yusuf Gawuna Gwamnan 2015 insha Allahu. Allah ya amsa mana, domin Annabi Muhammadu (s.a.w). Daga Abduldadir Abbas Aliyu Limanchi Dala    

Ga Alh Musa Nashuni.
 Edita dan girman Allah ba ni fili inyi godiya ga Mallam Musa Nashuni Bawan Allah kan yadda ya dauki dabi’u da halayen shema mai albarka wajen kyautatawa jama’a da tabbatar da zaman lafiya. Mungode, Allah kai likafa gaba. Amin. Daga Amiru Isa Bakori, 08075959086.

Jinjina ga Sarkin Kano
Aminiya ku mida mini gaisuwa da jinjina ga jagoran Kanawa adalin Sarki mai koyi da fiyayyan hallitta Muhammad SAW, wato Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 2 da maigirma gwamna mai jiran gado Ahmad Garban Bichi da shugaban dasar gobe  danmaji dadin Kano hakimin Madobi Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso mai kishin Kano da  dasa baki daya .
Daga Musa Hausawa Kano

Ka yi daidai dangote
Assalamu alaikum Aminiya a mida min godiya. a wajen Aliko Gote na rage kudin Sumunti da ya yi. kuma ka yi daidai da bai shawarci kowa ba wajen yin ragin. Daga Abdulshahid Ja’en Kano nagode.

Ga sanata Ningi
Sadona zuwa ga sanata Abdul Ahmad Ningi mu al ummar Bauchi ba ma tare da kai , domin ka shekara 15 kana shugabantar al’ummar Bauchi ta tsakiya, amma ba ta canza zani ba don haka ba ma son ka zama gwamna a Bauchi 2015 in sha Allahu sai APC, kuma sanatan Bauchi  ta tsakiya, santaral sai Shehu Barau Ningi in sha Allahu sako. Daga Manya Ningi 09030366586

Addu’a ga Najeriya
Salam. Allah Najeriya zaman lafiya Ameen   Daga Safiyya Ibrahim Magayadin Zazzau  dwarbai Birnin Zariya.

Addu’ar zaman lafiya
Edita ka isar min da sadona ga jama’ar Adamawa da Barno da Yobe da Gombe da fatan Allah ya kawo musu dauki da gagawa. Ameen. Daga Habeeb dangote Area2, Garki Abuja.

Zaben 2015
Edita Don Allah ka sanar wa al’ummarmu  cewa zaben 2015 da za a yi lallai mu dage,kada mu zabi wadanda za su ci gaba da zubar da jinin al’umma. Domin shugaban duk da ba adali ba ne, ba zai iya jan ragamar al’umma ba. Daga Yahaya Ahmed Jabo, Apapa Lagos 08026392800.

Ga jam’iyyar APC
Don Allah Edita a ba ni dama in ja hankalin shugabanninmu,  musamman na Apc., wajen zaben fitar d agwani. Ba girmanku ba ne, Tambuwal da kwankwaso ko Buhari wani daga cikinku ya janye kawai. Ku mara wa daya daga ciki baya amma kunzo zakuja rarrabuwar kawuna. Sai  kuma wasu shugabannin da suke magana ba kai ba gindi, su ma su kula jama’a ba gumaka ba ne, da za a ce wai a buge su. To tambaya a nan idan aka buge su su ba su da hannun ramawa ne? Daga  Isma’il Lawal dandara. 08032619334.