✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina barayin suke? (4)

Na san zai yi wahala mu iya amincewa cewa yawancinmu barayi ne kamar yadda shugabanninmu suka kasance barayi bisa tunanin da Alhaji Balarabe Musa ya…

Na san zai yi wahala mu iya amincewa cewa yawancinmu barayi ne kamar yadda shugabanninmu suka kasance barayi bisa tunanin da Alhaji Balarabe Musa ya rattaba mana. Haka zai yi wahala mu iya yarda cewa mu ma lalatattu ne, ko macuta ko mahandama ko kuma wani abu makamancin haka. Ba kuma wani abu ke jawo haka ba sai ganin wani bangare na rayuwarmu da ya dabaibaye rayuwa baki daya, ya hana mu sakat, wato kasancewa makaryata. Dukkkan al’ummar da kuma ta dage ganin karya a matsayin albarkar rayuwa to ba abin da take nema wa kanta sai faduwa kasa riris.
Saboda haka idan mu duka tun daga yara kanana da ke fara koyon tarbiyyar rayuwa zuwa karshen baligai da ke cikin kasar muka amince mu daina yi wa kanmu karya, sa’annan muka sha alwashin ba za mu kara yin cuta da cutarwa ba. Ba za mu kara yin sata da sacewa ba. Ba za mu kara yin handama da handamewa ba. Ba za mu kara yin mugunta da mugun hali ba. Ba kuma za mu kara karya doka da dukkan ka’idojin gudanar da lamurran rayuwa ba, ina da yakinin cewa rayuwarmu za ta canja. kasarmu za ta hau sabuwar turbar da har abada ba za mu koma baya ba, sai dai gaba!
Ta yaya hakan zai kasance? Mu dauko misali daga cikin gida, daga harabar garka da mazaunin iyali. Idan iyaye suka kasance na kwarai, suna tarbiyyar ’ya’ya bisa ingantaccen tsari na son gaskiya da rikon amana da guje wa duk wata lalatattar rayuwa, ’ya’yan nan nasu za su tashi cikin rayuwa tagari, za su kasance masu bin doka da oda wajen gudanar da rayuwar yau da kullum. Da wuya ka sami irin wadannan ’ya’ya cikin hada-hadar satar jarrabawa tun suna kananan makarantu har zuwa jami’a. Da wuya su samu kafar da za su shiga cikin al’amuran almundahana da cin hanci da babakere. Idan har sun mike cikin tadoji na kwarai, ba su sha cuta da cutarwa a cikin nonon mahaifa ba! Ba su ci daga cikin abincin haram da haramiya ba! Ba su sa tufafin da aka saya daga dukiyar bataccciyar hanya ko makauniyar kasuwa ba! Ba su kuma yi wanka ko kurme cikin ruwan fitsara da wulakanci ba, irin wadannan ’ya’ya in sun girma za su kasance abin alfahari da godo ba ga iyayensu kadai ba, har ga al’umma baki daya.
Wani karin haske dangane da wannan misali shi ne, al’ummar da ta gina rayuwar matasanta cikin wannan yanayi na son gaskiya da rikonta komai kunci, sa’annan sauran azuzuwan da ke cikin kasar da kuma al’ummomi mabambanta suka kasance su ma na kwarai, suna ayyukan kwarai, sa’annan suna kira ga yin ayyukan kwarai da wuya ta kasance batattar al’umma, domin kuwa ba inda aka bar kafar da za a yi barna a cikin kasar. Misali, matashin da ya mike da son gaskiya da alkintar da ita, ya shiga cikin al’umma ya same ta da ’yan kwadago masu kishin kasa da malamai (na addini da na boko) masu bin tafarkin gaskiya. Haka kuma ya sake watayawa a cikin kasa ya samu wannan al’umma da talakawa masu son gaskiya da kare ta, ya ci karo da masu sana’a babu algushu ko neman riba ido rufe, ya kasance ya shiga cikin hada-hadar neman aiki ya ci karo da shugabannin kamfanoni da masana’antu da ofisoshi ba sa bautar komai sai gaskiya da rikon amana, ba Naira ko son rai da annamimanci ba, duk yadda yake son ya kasance mugun iri, sai ya auna da kyau ya ga in akwai riba a cikin irin wannan sana’a da yake son ya fada cikinta. Kuma na tabbata sikelin da zai yi awon ba zai masa karya ba, domin zai nuna masa gaskiya daya ce, ba ta bukatar kwalliya.
Ke nan idan matasa suka mike cikin son gaskiya da bin tafarkinta, suka kuma iske yawancin al’umma na bin wannan turba, sa’annan uwa-uba shugabanni ta kowace fuska muka dube su, su ma suna shuka gaskiya da girbar ta, da wuya wannan al’umma ta yi ragon azancin rayuwa da wuya kuma ta yi barin cikin da ta dauka wata tara mai dauke da ’ya’ya nagari. Idan gwamnati da shugabanninta kuma suka zamo jagororin wannan tafiya, suka yi guzurin kwarai da madugai da ba sa tsoron jan ragamar rakuman da ke biye musu da ladabi da biyayya, sa’annan suna tafe da ayarin yakin zalunci da danniya da babakere da cuta da cutarwa, to da wuya a ce irin wannan al’umma ba za ta kai gaci ba!
Ashe ke nan gyara kasa da al’umma irin tamu duk da cewa ana ganin abin da kamar wuya, yana iya faruwa, ko yau ko kuma gobe, in dai an sa ran ana son canjawa. Ba kuma komai ake bukatar canjawa ba face ni na canja, ke ki canja, shi ya canja, ita ta canja, duk mu canja, daga sama har kasa, kasarmu kuma za ta canja, canji kuma wanda kowa zai iya ji da gani!
kila wasu su ce ta yaya za a canja a irin wannan hali da yanayi da muke ciki? Ta yaya za a iya gyara dankalin da na ce ya riga ya kamu da ciwon sankara? Ta yaya za a iya samun wani abu ko da kyas ne mai kyau daga jikin dankali mai sankara, har ya zama an lasa a baki? Wannan abu mai sauki ne. Ba inda aka fara fafutikar kawo canji da aka samu canjin nan cikin kwana daya ko biyu ko shekara daya ko biyu. Fafutikar neman sauyi daga lalatacciyar rayuwa irin tamu, dan ba ne ake azawa, babbaku da farfaru da karatun alhalari da ishimawi da manyan littattafai su ke biyowa baya, daga haka ake samun gardin Malami ko kuma Shaihi, wanda ke cike da ilimi na kwarai da zai karantar zuwa ga tafarki na gaskiya. Tambayar ita ce, mun shirya sa dan ba domin kawo canji ga wannan lalatacciyar rayuwa tamu? Ni dai na sa, daga yau ba na kara sata ko bin tafarkin da ba na gaskiya ba! Ku fa?

 Mun kammala