✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na yi farin ciki kan dawo da buga jaridun Daily Trust a Borno – Zulum

Gwamnan jihar Borno da ke Arewa Maso Gabashin Najeriya, Babagana Umara Zulum ya bayyana muradinsa na ganin an dawo da ci gaba da buga jaridun…

Gwamnan jihar Borno da ke Arewa Maso Gabashin Najeriya, Babagana Umara Zulum ya bayyana muradinsa na ganin an dawo da ci gaba da buga jaridun Daily Trust da Aminiya a jihar.

Gwamnan, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba da daddare yayin da yake bayyana farin cikinsa da dawowar madaba’ar a hedkwatar jihar ta Maiduguri bayan isowarsa madaba’ar da ke kan titin Baga da misalin karfe 9:00 na dare tare da Babban Jami’in Zartarwar kamfanin Mallam Mannir Dan-Ali da sauran ma’aikatan kamfanin.

Ya ce, babu shakka yana alfahari da kamfanin wanda dawowarsa zai samarwa mutane da dama aiki tare da taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin jihar, inda ya kara da cewa mafi yawan mutanen Najeriya musamman na jihar Borno na matukar alfahari da jaridun.

Sannan a karshe ya jinjinawa kamfanin inda ya bukaci da su ci gaba da kula da wurin tare da amfani da kayayyakin aiki kamar yadda suka saba.

Wani sashin da ake buga jaridun Daily Trust

“Muna matukar nuna godiyarmu sannan kuma zamu ci gaba da ba ku dukkanin goyon bayan da ya kamata.” In ji shi.

Bayan nan ne Babban Jami’in Zartarwar kamfanin, Mannir Dan-Ali ya zagaya da shi tare da yi masa bayanin yadda ake gudanar da aiki a madaba’ar har zuwa fitowar jaridun, inda a karshe ya bashi kyautan kwafin jaridun da aka kammala bugawa a madaba’ar.

Madaba’ar jaridun Daily Trust da Aminiya da ke Maiduguri ke samar da kwafin da ake rabawa a jihohin Arewa-Maso-Gabas.